Ankama Mutane Uku Da Kan Mutum A Gombe
Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke mutanen 3 ne a yau Alhamis, a kauye Dinawa dake karamar hukumar Kwami ta jihar Gombe.
Mutanen da cafke dauke da kan mutum wanda ba a dade da yanke shi ba Mutanen, Sune:, Yale Sale mai shekaru 27 da Baba Muhammadu mai shekaru 24 da kuma Aminu Salisu mai shekaru 22 dukkansu mazauna Dinawa.