Labaran Yau

Kungiyar Kwadago NLC Zata Shiga Yajin Aiki Sati Mai Zuwa

Kungiyar Kwadago NLC Zata Shiga Yajin Aiki Sati Mai Zuwa

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta shirya tsaf domin fara yajin aiki a fadin kasar nan a ranar 2 ga watan Agustan 2023. Kungiyar ta NLC ta bayyana cewa ba za ta iya nade hannayenta ba yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da matsalar cire tallafin da ya kai ga gazawar gwamnatin Bola Tinubu wajen cika muradai da gwamnatin da kungiyar suka amince da su a kwanan baya, dalilan sune za su kai ga yajin aikin.

Kungiyar Kwadagon NLC ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta cika duk wasu manufofin da ake dauka domin jama`ar kasa ko kuma ta fuskanci yajin aikin da kowa da kowa zai shiga daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2023.

Saboda haka, kungiyar ta NLC ta umurci dukkan rassanta da majalisun jihohi da su gaggauta fara hado kan ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya, da fara shirin yajin aikin gama-gari, domin gwamnati ta gaza kawo tsarukan da zasu kawo wa talaka saukin rayuwa bisa ga wahalar da ake fama da ita bisa Karin kudin man fetur da ke azabtar da `yan kasa.

DOWNLOAD MP3

A cewar wakilan mu, wannan na daya daga cikin shawarwarin da aka cimma a taron kwamitin tsakiya na NLC da aka gudanar a ranar Talata, 25 ga watan Yuli a gidan ma’aikata na Abuja.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar NLC ta yi wa gwamnati mai ci barazanar daukar matakin yajin aiki. A watan Yuni ne dai gwamnatin Bola Tinubu ta kulla yarjejeniyoyin kusan guda bakwai da kungiyoyin NLC da Trade Union Congress (TUC) bayan gwamnatin tayi galabar dakatar da yunkurin kungiyoyin na tafiya yajin aikin.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button