Labaran Yau

Portable Ya Mika Kokon Baransa Wa Davido Dan Suyi Waka

Portable ya mika kokon baransa wa davido dan suyi waka

Mawakin legas Habib Okikiola wanda aka fi sani da Portable, yana rokon tauraron mawakin Najeriya Davido da suyi waka tare.

A baya in ba a manta ba, yayi wa mawaka guda biyu magana, wato wizkid da burnaboy da su yi waka tare wanda hakan bai kawo haske cikin duhu ba.

Bayan wannan rokon da yayi wa mawakan wizkid da burnaboy magana Kuma abin hadu ba a Twitter, Sai ya koma Instagram inda ya roki davido ya bashi ko baiti daya.

Bayan ya manna bidiyon da yafito yake rokon wanda ya nuna har chorus din wakan yayi, Sai kuma ya bayyana hotunan tattaunawansu da sukayi ta murya.

Mai taken wahala musik ya rubuta a shafin sa cewa mai kudin Ogun ka kyautatamin da baiti daya. Ya ce wanda zai taimakeka bare dameka ba.

Davido ya amsa da lakanin mawakin zaa zuu!

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button