Labaran YauNEWSPolitics

Dalilai Goma Da Suka Sani Ayyana Takara 2023- Osibanjo

Dalilai Goma Da Suka Sani Ayyana Takara 2023- Osibanjo

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya lissafo Dalilai  10 da suka sa shi ayyana takarar shugaban kasa a zaben 2023.

A ranar Litinin ne, Osinbajo ya ayyana takarar shugaban kasa a hukumance a cikin wani faifan bidiyo da ya saki a shafinsa ta Facebook.

Ya ce yana neman tsayawa takara ne a karkashin jam’iyyar APC, wanda ya bi sahun Bola Tinubu da Ministan Sufuru, Rotimi Amaechi da Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabe Umahi da kuma Gwamnan Jihar Koji, Yahaya Bello.

Mataimakin shugaban kasan ya yi wa yen Nijeriya alkawari guda 10 idan har suka ba shi damar shugabancin kasar nan.

Osinbajo ya bayyana cewa kwarewarsa da jajircewarsa za su amfani Nijeriya da kuma yen Nijeriya.

Ya ci gaba da lissafto hujjojin da suka sa shi nuna sha’awar takarar, inda ya fara da cewa Idan Allah ya kaddara tare da yardar mutanen Nijeriya suka ba ni damar shama shugaban kasa, zan kammala duk abubuwan da na fara.

Zan zamanantar da harkokin tsaronmu ta yadda za a samu kwarewa, sannan zan sauya tsarin shari’a na adalci ta hanyar inganta albashin ma’aikatan shari’a da jin dadinsu wajen tabbatar da adalci ga kowa da kuma kulawa da tsarin dokokin kasa, zan bunkasa ababen more rayuwarmu, musamman wutar lantarki da hanyoyi da titunan jirgin kasa da harkokin sadarwa.

Zan samar da kyakkyawan muhalli wajen gudanar da harkokin kasuwanci da bunkasa harkokin noma zuwa mataki na gaba, musamman samar da na’urori da inganta gonaki ta yadda za su kara daraja ta yadda gwamnati da ma’aikatunta za su dunga kulawa da harkokin kasuwancin, da kirkiran ingantaccen tattalin arziki da zai samar wa miliyoyin mutane ayyukan yi da inganta shirin bunkasa zamantakewa domin ya kasance shirin bayar da jin kai, da cika alkawari na tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10, da kammala aikin tabbtar da dukkan ‘yan Nijeriya maza da mata sun samu ingantaccen ilimi, da sake sauya tsarin harkokin ilimi da ta dade tana addabar kasar nan.

Zan kammala shirin samar da kiwon lafiya na bai daya ga kowa, da karfafa ayyukan jihohi da kananan hukumomi ta yadda za su iya gudanar da ayyukan da ya rataya a kansu.

Zan yi kokarin samar wa matasa ayyukan yi.”

Osinbajo ya kara da cewa, “Za mu yi aiki tare da izinin Allah, cikin shekaru kadan za mu cika wa ‘Yan Nijeriya burinsu. Za mu gina tubulin da zai kai mu ga samun nasara. Muna bukatar samun ci gaba mai dorwa cikin gaggawa domin ceto kasarmu.

Ya kamata mu gina Nijeriya ta yadda mutumin Nnewi zai dinga ganin mutumin Gusau a matsayin dan’uwansa na jini, ta yadda macen da ke Warri za ta dunga kallon macen da ke Jalingo a matsayin ‘yan’uwarta ta jini, ta yadda za a samu soyayyar juna a matsayin kasa daya al’umma daya.

Ya kamata kabilunmu su zama daya ta yadda kowa za a yi masa adalci da garmama shi. Ta yadda za a dauki kowa a matsayin daya ba tare da nuna bambanci ba a kasar nan,” in ji shi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button