Crystal Palace 0 – 1 Arsenal: Martin Odegaard Ya kwaci Arsenal A Gidan Crystal Palace
Golan Crystal Palace “Sam Johnstone” ya kwashe dan wasan Arsenal “Eddie Nketiah” da hannayen sa a cikin gaban raga, wadda yasa alkalin wasa ya basu ‘bugun kai tsaye da gola'(penalty) a minti 60 na wasan.
“Martin Odegaard” ne ya hau ‘bugun kai tsaye da gola” (penalty), inda ya kori golan a hanun dama, shikuma ya buga kwallon ta hagu a kasa.
A minti 67 ne dan wasa Arsenal me tsaron gida “Takehiro Tomiyasu“ ya samu jan kati, bayan yelon kati na farko daya samu a minti 60 saboda ya bata lokacin wasa, sannan yasamu yelon kati na biyu a ketan dayayi wa “Jordan Ayew” har ya kaishi kasa.
Arsenal sun tafi da maki uku a wasan, bayan hare-haren da su biyun suka yita kaiwa juna amma ba’a samu wadda ya sake jefa kwallo a raga ba a cikin su.
Arsenal sun ci wasan su duka guda biyu na farkon Premier league a wannan zangon. Crystal Palace kuma sunci wasan su na farko wadda suka buga da Sheffield United (1-0), amma basu samu nasarar cin wasa na biyu bah, hakan yasa suka koma na 11 a Premier league table.