AddiniLabaran Yau

Watan Musulunci, Ma’anarsu Da Kuma Faidodi

Watan Musulunci, Ma’anarsu Da Kuma Faidodi

Musulmai a fadin duniya Suna amfani ne da watan musulunci wajen tafiyar da rayuwar Ibadah da Kuma koyi da Ma’aiki Annabi Muhammad SAW, Kuma wannan kalandar ita ake kira Islamic Calendar.

Ita kalandar musulunci kalanda ne wanda ke sauyawa da yanayin wata, ita kalandar daban ta ke da na Gregorian wanda ta ke sauyawa da yanayanin rana. Kuma Tana farawa ne da Watan Junairu ta kare da Watan Disamba.

Islamic Calender
Islamic Calender

Kalandu guda biyu kullum daga shekaru aru aru Suna banbance. Ko wani watan musulunci na da ma’anar sa a nashi yanayin da kuma ibadun da akeyi wanda wasu wajibi ne kamar Azumin Watan Ramadana.

Kalandar ta na da watanni guda Goma sha biyu na shekarar 1442 Bayan hijra.

Ga bayanin watannin wanda zasu zo a jere da muhimmancinci su da ma’anarsu.

WATAN MUHARRAM

Wannan wata itace watar farko a watan kalandar musulunci, sabuwar shekara ta zagayo Ana shiga watan Muharram.

Asalin Ma’anar watan Muharram daga harcen larabci shine abinda aka haramta, sai yasa aka haramta yaki ko kashe kashe a harami, a goma da sha 11 ga wata akanyi Azumin Ashura wasu sukanyi tasu’a.

WATAN SAFAR

Wannan watan musulunci na biyu kenan, Tana da ma’anar larabci Safr wato Gibi ko Damuwa saboda dashi.

Cewar a lokacin jahiliyya Ana kiran wannan lokaci haka saboda gidajen larabawa babu abinci, bayan masu kudin su sun tara dayawa.

A wani bayanin yazo da cewa Suna diban ganimar dukiyoyinsu bayan ci mutanen da suke samun matsala da a yaki, basu barin komai.

WATAN RABI AL-AWWAL

Wannan wata na uku kenan cikin watannin kalandar musulunci. Rabi al-awwal kalmar larabci ne wanda ke nufin Bazara.

Sunan Tana nufin lokacin kiwo saboda shanu Suna fita neman abinci kamar ciyawa a wannan watan.

Rabi’al-Auwal wata ne mai muhimmanci wa wasu musulmai saboda suna murnan haihuwar Manzon tsira mai suna Maulidi. A watan suka amince da cewa aka haifi Annabi SAW.

WATAN RABI AL-THANI

Wannan itace wata na hudu a watannin musulunci wanda ke nufi bazara ta biyu.
Wasu Suna kiranta da Rabi al-akhira wata Tana nufin bazara tazo karshe.

WATAN JUMADA AL-ULA

Watan biyar na watan musulunci, kalmar larabci ne wanda ke makale da ma’ana busasshiyar kasa. Kamin Zawan musulunci Ana kiranta lokacin iska da sanyi.

Wannan lolaci yakan zo ne a Wannan wata.

WATAN RAJAB

Wannan wata na bakwai a watannin musulunci, kalamar larabci ne rajab wanda ta ke nufi girmamawa.

A wannan watan an haramta yaki, shine wata na biyu da aka haramta yaki.

RAJAB ta na iya nufin cire abu, saboda a watan yan jahiliyya suna cire kan takwabinsu su ajiye saboda kar suyi yaki.

WATAN SHA’ABAN

Wannan wata ta Sha’aban wata ne Na takwas na watannin musulunci, wanda ta ke nufi watsewa ko bajewa.

A wannan watan ko wani shekara larabawa suke watsewa su ba zama neman ruwa.

Sha’aban Kuma ta kan fito da ma’ana “zama tsakiyar abu biyu” saboda watan Tana tsakiyar watan Rajab da Ramadan.

WATAN RAMADAN

Wannan watan tara ne na watannin musulunci wato watan Ramadan. Watan Ramadana watane wanda yafi sanuwa acikin sauran watannin musulunci a duniya.

Kalmar larabci ta Ramadan tana nufin “tafasan zafi”

Tafasa Tana da alaqa da azumi da cikin Mai yunwa hakan yake kona wani dogon buri.

Da zafin rana mai sauka a wannan watan da zafi Mai yawa, Ramadan itace watan da ta fi ko wani wata zafi a kalandar bayan hijra ta musulunci.

A wannan lokacin ake so musulmi yayi azumi daga tasowar rana zuwa fadowar rana. Kuma da taimaka wa wanda basu da hali.

Aikin Alkhairi da falala ta ke a watan Ramadan.

Muhimman Ibadodi Guda Biyar Cikin Watan Ramadan

1- Salloli: Wannan wata na Ramadan yana da salloli na nafila masu yawa da aka ruwaito,da farko akwai sallar nafila raka’a dubu,malamai sun yi bayanin fuskoki na yin wannan sallah, amma fuskar da tafi shahara itace: kowane dare bayan mutum yayi sallar magariba da nafilarta,sai yayi raka’a 8,bayan yayi sallar Isha’i da nafilarta sai yayi raka’a 12.

Haka zai ta yi kowane dare,wato tun daga daren farko har ya zuwa daren 20.

To a daren goma na }arshen watan Ramadan,8 da ya saba yi bayan sallar magariba tana nan,amma na bayan sallar isha’i yanzu zai dun ga yin 22 ne maimakon 12.

To a daren 19,21 da kuma 23,to zai yi raka’a 100 wato baya ga sallar da ya saba ta bayan magariba da kuma bayan isha’i.Idan mutum ya lissafa su baki daya zai ga 1000 ne,wannan itace sallar Asham a mahangar Ahlul bayt.

Haka nan baya ga wannan sallah ta raka’a 1000 to kowane dare yana da sallar da ta ke~anci daren,idan aka duba cikin mafatihul jinan  za a gansu da dai sauran sallolin nafila da ake son yi a wannan wata mai albarka.

2- Karatun Al Qur’ani: Wannan wata na Ramadan ana so mutum ya yawaita karatun Alqur’ani a cikinsa,in son samu ne a duk kwana ukku mutum ya sauke,wato kullum yayi izu 20,in kuma haka bai samu ba to sai yayi abinda ya sauqaqa, fata dai mutum yayi sauka a cikinsa fiye da sauran watanni.Haka nan kuma ana son mutum ya karanta suratul qadri wato Inna-anzalnahu sau dubu kowane dare.

Haka nan ana son mutum ya karanta suratu-Dukan shima kowane dare na watan Ramadan da dai sauransu.

3- Azkar: Ana so mutum ya yawaita zikirori a watan Ramadan kamar su hailala,tasbihi,istigfar,salatin Manzon Allah da dai sauransu.

Wato dai mutum ya yawaita azkar a cikin watan fiye da sauran watanni,saboda wata ne da ake nunnuka ayyuka na bayi,kuma watan Ramadan fursa ce zahabiyya da bai kamata mutum yayi wasa da ita ba, kuma mutum bai sani ba ko wannan shine watan Ramadan na qarshe a rayuwarsa.

4-Addu’oi: Wannan wata na Ramadan yana da addu’oi ma’asurai fiye da sauran watanni,kuma wa]annan addu’oi akwai wa]anda ake yin su da daddare, akwai kuma wadanda ake yi da rana,akwai kuma wadanda ake son yinsu bayan kowace sallah ta farilla, akwai kuma wa]anda ake yi bayan kowace raka’a biyu ta nafilfili dubu da aka ambata a sama,akwai kuma wa]anda ake yin su lokacin as-har wato kafin ketowar alfijir da dai sauransu.

To ana so wa]annan addu’oi baki ]aya mutum ya lizimci yinsu tun daga farkon watan Ramadan har qarshensa,kuma wannan abu mai yiyuwa ne,misali mu dauki addu’ar da tafi su tsawo duka a watan,wato Addu’ar Abu Hamzatus-sumali wanda ake karanta ta a lokacin Ashar, to akwai bayin Allah da suka haddace ta,kowane dare da ita suke }unutin sallar wutiri.

A takaice ga mai buqatar ganin wa]annan addu’oi dabam-dabam da ake yi a watan Ramadan yana iya duba littafin I}bal na Sayyid ibn Qawus ko mafatihul jinan da dai makamantansu.

 5- Ziyarori: Mustahabbi ne ziyarar Imam Husain[AS] daga kusa ko nesa a daren farko na watan Ramadan,da daren sha-biyar da kuma daren karshe.

Haka nan ziyarar Imam Ali [AS] a daren 21 da dai sauransu.Yin wa]annan ziyarori a irin wa]annan munasabobi yana da falaloli da kuma fa’idodi masu yawa,daga cikin wa]annan fa’idodi shine yana da]a kusanta mutum ga Manzon Allah da kuma Ahlul bayt [AS].

WATAN SHAWWAL

Watan shawwal watan goma ne cikin watan musulunci. Tana da kalmar larabci wanda ta ke nufi “dagawa ko tashi”.

Taguwa Suna kanana mafi yawan lokaci a wannan watan suke daga jelan su.

WATAN DHUL QA’DAH

Wannan shine watan goma sha daya a watan musulunci, kalmar larabci ce wanda take nufin an shirya ko zama.

Wannan wata ne mai tsarki, a watan aka hana yaki amma ka kare kanka in an kai maka farmaki.

WATAN DHUL HIJJAH

Watan sha biyu, watan karshe kenan na kalandar watannin musulunci wanda ya fara da Muharram. Kalmar larabci ne wanda ta ke nufin lokacin hajji tayi.

Musulmai na fadin duniya zuwa suke kasar saudiyya dan yin aikin hajji ga wanda Allah ya kira.

A watan ake aikin. Hajji yayin da mutane suke zuwa dawafi a ka’aba na cikin garin Makkah.

Anayin aikin hajjin ne a ranar 8, 9 da 10 na watan DHUL hijjah. Ana hawan Arafat ranar 9 ga watan. Sai ayi sallar laiya a ran goma ga watan a gama a ran 12 ga watan rana tana faduwa. Lokacin da aka hana yaki.

Bidiyon Nasheed Na Months A Islam Shine Daga Bisani ⇓

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button