Ma’aurata biyu Sunyi Garkuwa da kansu dan kudin Fansa Miliyan biyar
Kwaman din yan sanda Na jihar legas sun kama ma’aurata kan garkuwa da kansu dan samun kudin fansa miliyan biyar.
Mai magana da yawun kwaman din Benjamin Hundeyin, ya bayyana lamarin wa Hukumar labarai ta kasa ranan Asabar.
Hundeyin, sufirtandan yan sanda yace Mutumin shakarsa hamsin da uku da matarsa Yar skekara arba’in da takwas an kamasu ran laraba da Alhamis bayan iyalinsu sun bayyana lamarin garkuwan.
Yace ma’auratan sun fadi cewa su sukayi da kansu dan su siya bayan gidansu a badagry akan naira miliyan uku.
“Ya bayyana yin garkuwa da kansa dan yan uwansa masu hali da wanda suke kasar waje basu iya kyautata masa da kudi.
“Yace in sukaji anyi garkuwa dashi da matarsa zasu yi magana Kuma su bada kudaden dan a sake su” jami’in ya bayyana.
Hundeyin yace suna zaune a gidan su bayan sun tura sakon garkuwa da akayi dasu, ranan talata yan sanda sunje sun tarar da matan da yayanta guda uku, sukayi kokarin tafiya da ita inda ta nemi zata je ofishin da kanta ran laraba, Kuma suka yarda.
Takai kanta bayan alkawarin da tayi na zuwa Kuma ta fadi cewa ta amince suyi garkuwa da kansu bayan mijinta ya kawo batun. Washe gari Alhamis mijin ya shiga hannun yan sanda.
Ta bayyana cewa sunyi hakan ba tare da tunanin zai iya fashe musu ba, saboda inda hakan ya yiwu da sun samu hanyar sauki na samun kudin dan siyan bayan gidan su tunda yan uwansa na burtaniya basu taimaka masa cewar matar.
Mista Hundeyin yace yaji mamaki dan matar Tana tausan jiki kuma Tana samun dubu dari da hamsin kan kowani mutum daya wanda har barata iya tara musu kudin ba.
Duk da dai sun nuna nadamar su nayin hakan, Kuma suna neman yan uwansu da yan sanda da su yafe musu.
Ya kara da Jan kunnen mutane da su cire idanuwansu akan dukiyan yan uwansu. Kuma za a kaisu kotu.
Daily Nigeria ta rawaito