Labaran YauNEWSTrending Updates

Zanga Zangan Zai Iya Jawo Karin Wahala: Kungiyoyi A Kudu Sun Janye Daga Shirin Zanga Zangar 1 Ga Wata

Manyan kungiyoyi a kudancin najeriya sun hada kai don janye shirinsu na yin zanga zangan lumana

A yaune 25 ga watan yuli, manyan kungiyoyi a kudancin najeriya suka sanar da cikakkiyar janyewansu daga shirin zanga zangan lumana da za a fara 1 ga watan augusta 2024.

Kungiyar Rivers Good Governance Coalation, wato ma’ana kungiyar hadin guiwan tsaftacecciyar gomanati na garin Riverse sun nuna janye ra’ayin nasu ne bisa da tunanin rashin tasirin zanga zangan wa neman mafita.

kamar yanda labari yazo dashi cewa shugaban kungiyar ya jaa hankalin matasa akan su la’akarin janye zanga zangan dan babu amfaninshi a wannan yanayi.

Yace ra’ayinsu ya samu babbar sila ne daga wurin ma girma gomna Siminalayin Fubura bayan basu shawari na basira da kara wayar musu da kai kan illar zanga zangar.

Shigan gomnan jihar Rivers din yayi tasiri sosai wurin jawo hankalin manyan kungiyoyin, ya basu shawarwari da tabbacin hadin kai wurin kokarin bin hanyoyi masu sauki dan shawo kan lamarin.

Kungiyar ta kara da jan hankalin matasan kasa masu shirin gudanar da zanga zangan kan cewa su zauna su kara nazari kan kare lafiyansu dakuma ta al’umma. Kar fushi ta ja niyyarsu wurin tafka kuskure.

kuma kungiyar tana kara jaddadawa akan cewa lallai zanga zangan zai iya jawo karin wahala da kunci fiye da samun mafita.

Shugaba Tinubu kan zanga zangan

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana ta jajircewa gurin ganin yajawo hankalin matasa kan rashin bukatan yin zanga zangar, yana kuma kara tabbatar wa matasa kan cewa yana nan ba dare ba rana wurin samo hanyan kauce wa da kuma samun mafita wa ‘yan kasa.

Maganan Tinubu ya tabbata ganin irin abubuwan da yake aiwatar wa a cikin kan kanin lokacin dan saisaita zuciyan matasa da sauran yan kasa gaba ki daya.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button