Labaran Yau

JAMB: Kampanin Innoson Ta Bada Ka’idojin Janye Tallafi Wa Ejikeme

JAMB: Kampanin Innoson Ta Bada Ka’idojin Janye Tallafi Wa Ejikeme

Kampanin Kera mototi na Innoson, Ta ce tallafin karatu na Miliyan Uku da ta bawa Mmesoma Ejikeme yana nan in har an gano cewa bata da hanu cikin laifin da Hukumar jarabawa Ta Jamb ta ke zargin ta da shi na canza sakamakon ta.

Cornel Osigwe, Shugaban sadarwa na kampanin Innoson ya bayyana wa Hukumar labarai ta kasa ran litinin a garin Onitsha.

Hukumar jarabawa ta jamb, Tana zargin Ejikeme da amfani da na’urar computer wajen canza sakamakon ta zuwa 362 daga 249.

Ejikeme

Bayanin Osigwe, abu ne Mai ban mamaki kan sauraran jamb Tana fadin cewa Ejikeme ta canza sakamakon ta.

“Abin mamaki ne cewa ita ce ta samu mafi maki dayawa, Mun jira jamb ta zo ta bayyana mana Gaskiyar magana amma basuyi hakan ba, Kuma an bayyana a media cewa ita ce gwarzuwan shekarar.

“Kuma mun jira muga ko za a samu wani bayani ko karyata hakan na wani lokaci Amma babu, hakan yasa muka bata tallafin karatu a matsayin ta na gwarzuwan shekarar.

“Ranar lahadi Hukumar Jamb ta bayyana cewa ta canza sakamakon jarabawan ne. Muma Muna namu binciken dan mu gano gaskiyar lamarin ko ita tayi hakan ko matsalar Jamb ne.

“In Mun gane cewa yarinyar ita ta canza sakamakon jarabawa ne dan ta samu tallafi, Zamu janye tallafin.

“Amma in Mun gane cewa matsalar daga jamb ne, Kuma in sune suka bada sakamakon a hakan, Kuma sakamakon nata yana 249 Zamu bata tallafin”

Osigwe ya bawa Ejikeme shawara kar ta daga hankalin ta, cewa Suna da karfin da zasu yi nasu binciken dan su gano gaskiyar lamarin.

Ya kara jaddada cewa in sun gano bata da hannu cikin matsalar, ko taci ko bata ci ba, tallafi za a bata.

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button