Labaran Yau

Gwamna Namadi Ya Tura Sunan Kwamishina 16 Wa Majalisan Jiha

 Gwamna Namadi Ya Tura Sunan Kwamishina 16 wa Majalisan Jiha

Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya mika sunayen kwamishina 16 wa Majalisan jiha dan tantancewa da amincewa.

Sunayen ya kunshi sunayen kwamishinan da sukayi aiki a gwamnatin da ta gabata karkashin Muhammad Badaru Abubakar.

Hakan yazo jikin bayanin da Bala Ibrahim, sakataren gwamnatin jiha, ran talata a Dutse.

“Ina fatan tantancewar zai samu goyon baya da Kuma duba wajen yan majalisun jiha” a bayanin da Namadi yayi cikin wasikar da ya tura wa yan Majalisan jihar.

Wasikar ta bayyana neman da gwamna yakeyi dan tantancewa da amincewa yana daidai da dokar kasa sashi 192 na dokar 1999 wanda aka gyara.

Sunayen da aka tura ya kunshi: Ibrahim Babangida Umar, Farfesa Hannatu Sabo, Dakta Muhammad kainuwa, Aminu Kanta, Ahmed Garba, da ibrahim Hannungiwa.

Wasu daga ciki sun hada da, Dakta lawan Danzomo, Dakta Isa Chamo, Sagir Ahmed, Hadiza Abdulwahab, rtd col Muhammad Alhassan.

A cikin jadawalin sunayen akwai dakta Nura dandoka, Gambo Shuaibu, Auwal Sankara, Musa Adamu Aliyu, da muttaka Namadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button