Hukumar Zabe Ta Bawa Gwamnan Kwara Takardan shaidan cin Zabe da wasu 24
Hukumar Zabe a jihar Kwara ta baiwa gwamnan jihar Abdulrazak Abdulrahman da mataimakinsa takardan shaidan zabe da yan majalisun jiha guda Ashirin da hudu.
Anyi taron ne a babban birnin jihar lllorin ranan Talata wanda kwamishinan Zabe Farfesa Sanni Muhammad Adam ya bayar.
Shi farfesa ya yaba yanayin zaben saboda an aiwatar ne cikin lumana da zaman lafiya. Ya nuna cewa hukumar tsaro sunyi iya bakin kokarin su dan samar da nutsuwa tsakanin mutane a lokacin zaben da ta gabata.
Ya kara yabawa yan jaridu dayin aikin su daidai ba tare da sun fadi abinda zai tada tarzoma cikin mutanen jihar ba.
Gwamna Abdulrazak ya Mika godiyansa wa talakawa, dalibai, yan siyasa, ma’aikata,da sauransu dan basu daman cigaba da aikin da suka fara Kuma barasu watsa musu kasa a idanuwansu ba.
Ya jaddada cewar zaiyi aiki matuka dan yelwantuwa na jama’arsa, Kuma yana addua Allah yayi riko da hannunsa dan yin abinda ya dace a wannan Karo.