Labaran Yau

Babban Masallacin Tarayya Ta Abuja Ta Raba Abinci Wa Yan Hijira..

Ramadan: Babban Masallacin tarayya ta Abuja ta raba abinci wa yan hijira dari hudu

Gidauniyar da’awah da jindadi na babban masallacin tarayya ta raba abinci wa yan hijira musulmai guda dari hudu a garin Abuja.

Shugaban gidauniyan, Dakta Muhammad Kabir Adam wanda jagoranci sauran tawagar gidauniyar dan bada wannan kayan abinci wa yan hijira wanda keh mazaunin yan hijira wanda keh Area 1 da kuma dakin taro na babban masallacin tarayya.

Yace anyi hakan ne dan a taimaka wa wanda basu da shi da kayan abinci dan samun sauki a watan Ramadan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Kuma sun bayyana daya Daga cikin kudurorin gidauniyar inji cewar jafaru umoru.

Gidauniyar an kirkiro ta shekarar da ta gabata, murshidin masallacin farfesa shehu said galadanchi ya na kan da’awah da kyautatawa.
A wannan wata Ramadana suna hadakaiya da mutane da kungiyoyi.

Yace “ abinda muka bada shine abinci wanda ya kunshi shinkafa, semovita, man abinci, da wasu kayan girkin, Kuma Mun rabawa yan hijra guda dari daya a Area 1 Abuja.

Bayan haka Wasu daga cikinsu za’a basu tallafi da horaswa dan dogaro da kai da kuma zama wanda zasu iya aiki in an daukesu”.

Yayi gargadi wa masu hali da kungoyi wajen taimakawa a watan ramadana, Dan hakan bauta ne wa ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button