Labaran Yau

Asalin Dalilin Zuwan Shugaba Buhari Umrah | Haduwarsu Da Tinubu

Dalilin Zawan shugaba Buhari Umrah

Shugaban kasa Muhammadu buhari yaje kasa Meh tsarki Saudi Arabia don yin aikin umrah kuma da godiya wa Allah da niyyan mika karagar mulki wa shugaban kasa meh jiran gado Bola Ahmed Tinubu wanda za ayi ran 29 ga watan mayu.

Shugaban kasan ya bar Najeriya zuwa Saudi Arabia ran 11 ga watan Aprailu zuwa 19.

A bayanin mai maigana da yawun Shugaban kasa Shehu Garba, Yace tafiyar sa na karshe kenan a matsayin sa na Shugaban kasa.

DOWNLOAD MP3

Ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital farfesa Isa Ali Pantami da Shehu Garba sun bayyana hakan wa manema labarai akan dalilin da ya kai Buhari saudiyya, don godewa Allah da ya bashi ikon mulkan Najeriya na shekara takwas.

Shugaba buhari ya tafi tare da masu taimaka masa, sun fara shiga madina inda ya zaga wajen tarihi Na addini da dakin tarihin Annabi Muhammad da kuma inda aka fara samun waye wa da cigaba na addinin musulunci.

A wajen tarihin, ya bayyana cewa yana da muhimmanci a sanar da mutane addini a duniya gaba daya.

DOWNLOAD ZIP

Shugaban ya nuna muhimmancin bada ilimin addini a saukake inda ya bada shawaran kawo hanya mafi sauki dan yada ilimin addini da fahimta wanda shine abinda musulunci take da’awah akai.

Buhari yayi salloli biyar na ranan harda taraweeh a masallacin annabi kamin fitar sa zuwa Makkah ta hanyar jiddah ran laraba dan aikin umrah.

Shugaban kasan Najeriya yayi aikin umrah da mutanen sa wanda ya kunshi sarakunan gargajiya da sauransu.

Buhari ya yabawa dan kasuwa meh taimakon Aliko dangote ranan zagayowar haihuwansa na cika shekaru 66 da Kuma mishi adduan Alkhairi.

Yace dan kasuwan ya baiwa kasar Najeriya girma da kima a idon duniya.

Ya Kuma garzayawa zuwa ziyarta tsohon dan kasuwa Dantata a masaukinsa dan ta’aziyar rasuwan iyalinsa, Rabi Dantata wanda ta rasu ran 9 ga watan Aprailu 2023 a Saudi Arabia.

Shehu Garba ya bayyana jin rasuwan Rabi dantata ga buhari.

Buhari Yace marigayiya zata kasance a zukatan mutane dan kyautatawan da akan sa ta dashi da taimako.
Daily Nigeria ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button