Gwamnan Jihar Taraba yayi Alkawarin biyan giratuti
Gwamnan jihar taraba Agbu Kefas yayi alkawarin zai fara biyan giratuti na ma’aikatan jiha dana karamar hukuma da suka yi ritaya. Ya bayyana hakan wa manema labarai in jalingo cewa zai fara biyan kudin giratuti da fansho domin rage wahalan da mutane suka tsinci kansu na rashin biyan su hakkin su.
Kefas yayi maganar duba cikin yanayin fitar kudade na gwamnati wanda hakan yasa za’a kulle Duk kofofin da ake amfani dasu wajen satar kudin gwamnati.
Ya bada umurnin aikin shiga da fitar kudin gwamnati da duba wajen tabbacin gudanarwa.
In an tuna, satin da ya gabata kamin a mika karagar mulki, Hukumar kwadigo ta jihar taraba, tace gwamna Darius Ishaku ya riqe kudaden Yan fansho da giratuti naira biliyan Ashirin da biyu wanda ba’a biya ba. Kuma darurrukan malaman Makaranta dasuka yi ritaya ba a sanya su cikin tsarin fansho ba.
Hukumar kwadigo Tana zargin gwamnatin jihar taraba karkashin Darius cire kudade naira mikiyan dari takwas daga Albashin ma’aikata na gidaje da kudaden aro.
Daily trust ta rawaito