Labaran Yau

Sabuwar Ministar Mata Ta Yi Alkawarin Tallafawa Mata Manoma

Ministar harkokin mata, Misis Uju Kennedy-Ohanenye, ta jaddada kudirinta na karfafawa, noman karkara, da kiwon lafiya ga mata da yara a kasar nan.
Kennedy-Ohanenye ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da take gudanar da aiki tare da ganawa da manema labarai a Abuja.
A cewar ta, ma’aikatar za ta yi kokarin ganin ta magance radadin da mata da kananan yara ke addabar su, musamman inganta harkokin kiwon lafiya da kuma noma ga wadanda ke yankunan karkara.
Ta bayyana cewa, za a horas da mata a shiyyoyi shida na siyasa a kan sana’o’i daban-daban, wadanda za su kuma ba wa wasu don inganta rayuwarsu, da GDPn kasar, da magance barace-barace da rashin tsaro.
“Waɗannan abubuwa na daga cikin abubuwan da zan cimma daga yanzu zuwa kwana 100 a ofis kamar ƙarfafawa mata, koya musu sana’o’i, horar da waɗanda ake horar da su don ƙarfafa mu aƙalla mutum 10.
“Na yi niyyar fara horar da matan a shiyyoyi shida na kasa, inda za mu zabi jihohi, kuma nan kusa zamu yanke shawarar jihohin da za mu fara.
“Idan har za mu iya cimma hakan a cikin kwanaki 100, za mu nemo wadanda za su ba da gudummawar kayayyakin ga mutanen da aka horas da su su fara aiki da kwarewarsu, amma da sharadin kowannensu zai horas da mutum 10, wanda haka za mu ba su karfin gwiwa. ” ta kara da cewa.
Dangane da noman karkara, ministar ta yi kira ga jama’a da su daina amfani da mukamansu da alakarsu wajen kwace shirye-shiryen da ake yi wa wata kungiya.
” Idan muka tambayi mata manoman karkara kuka yi amfani da haɗin gwiwa ku kwaci abin da yake nasu alhalin kun san ba za ku je ƙauye don yin noma ba.
Sabuwar Ministar Mata Ta Yi Alkawarin Tallafawa Mata Manoma
Sabuwar Ministar Mata Ta Yi Alkawarin Tallafawa Mata Manoma
“Waɗannan wasu abubuwa ne da ba za mu amince da su ba saboda ina so in yi aiki da mata kuma in ga waɗanda ke fama da wahala, muna kallon su kuma muna taimaka musu,” in ji ta.
Don haka ta bukaci ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki da su marawa gwamnati baya wajen ganin ta cimma ayyukan ta domin ci gaban kasa baki daya.
” Ina so ku gane cewa ba ni nan don cin zarafin kowa ba sai dai idan ba ku shirya yin aiki ba.
“Na zo nan ne domin in zaburar da mata su yi aiki tukuru, in koya musu yadda ake kamun kifi da kuma kare ’ya’yansu da karamin karfin da Shugaba Tinubu ya ba ni, aikina ke nan,” inji ta.
Ministar ta kuma bukaci abokan hulda da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafawa gwamnati ta tsarin inshorar da zai baiwa mata da kananan yara a yankunan karkara damar samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Ta kuma yi kira da a ware akalla kashi daya cikin dari na harajin shaye-shaye, taba sigari da sauran su domin a samar da ayyukan kula da lafiya ga mata, musamman a yankunan karkara domin rage yawan mace-mace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button