
Tinubu Ya Maida Hukumar Jinkai( NEMA) Da Kwamishan Din Alhazai karkashin Ofishin Kashim
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dawo da hukumar jin kai na kasa (NEMA), zuwa ofishin maitaimakin shugaban kasa Saboda duban aiyukansu, Hakan yazo daidai da tsarin doka.
Shugaban kasan ya kara amincewa da dawowan kwamishan na Alhazai )National Hajj commission) ta kasa, zuwa ofishin mataimakin shugaban kasan Najeriya.
Olusola Abiola, daraktan zantarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa ya bayyana ran talata a Abuja.
Daily Nigeria ta rawaito cewa Tinubu ya amince da tsarin ofishin mataimakin shugaban kasa da Kuma yawan Ma’aikatan da zasuyi aiki a ofishin da taimaka wa shugaban wajen gudanar da aikin da ke rataye a wuyan shi.