Labaran Yau

Sojoji Sun Ceto Karin Daya Daga Cikin Matan Chibok

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun bayyana cewa sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok a jihar Borno. Yarinyar da aka ceto na daga cikin dalibai 276 da aka sace.

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun bayyana cewa sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok a jihar Borno.

Yarinyar da aka ceto na daga cikin ‘yan matan makaranta 276 da Boko Haram suka sace a ranar 14 ga Afrilu, 2014 a garin Chibok.
An bayyana hakan, jiya ta bakin kwamandan OPHK, Maj-Gen. Gold Chibuisi, yayin da yake mika Mary Nkeki ga kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Borno, Zuwaira Gambo a unguwar Maimalari dake Maiduguri.

DOWNLOAD MP3

OPHK
OPHK

Ya ce an ceto Mary, mai shekaru 27, a ranar 14 ga watan Agusta, 2023, an karbo ta daga hannun sojojin bataliya ta 81 na sojojin Najeriya, a garin Dikwa, gari da ke kan iyaka da Kamaru.
Cuta, da yunwa sun afkawa sansanin ‘yan gudun hijira na Benue, Gwamnatin Nasarawa ta haramtawa wadanda ba mazauna wurin ba zama a jihar

Ya kuma bayyana cewa sunan Maryam yana lamba ta 55 daga cikin jerin sunayen ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014.
“Dakarun sun ceto Maryam, yayin da daya Adamu; Mijinta ya mika wuya ga Sojoji a makon da ya gabata a yankunan kan iyaka da Kamaru,” in ji Chibuisi.

Wakilinmu ya tattaro cewa Maryam tana da jarirai guda biyu tare da mijinta, amma sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki. Maryam dai tayi rayuwa ne a hannun yan taddar cikin dajin Gulumba na karamar hukumar Bama.
Duk da ceto ta da aka yi, ta so ta sake haduwa da mijinta, Adamu, wanda tuni ya mika wuya a makon jiya a Dikwa.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button