Labaran Yau

An Sayar Da Mai Na Dala Biliyan 2.4 Ta Hanyan Da Beh Daceba A Shekaran..

Binciken man dala biliyan 2.4 da aka fitar ba farautar mayya bane cewar Gbajabiamila

Shugaban majalisan tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa an siyar da mai ta hanyan da beh dace ba a shekarar 2014 zuwa 2015, wanda akalla yakai kimanin ganga miliyan goma, an siyar a kudi dala biliyan biyu da digo hudu.

Ya ce hakan ba Farautar mayya bane Suna aikinsu ne na bincike akan abinda ya faru da man a gidan majalisan tarayya dake abuja ran talata.

A bayanin shi, bincike da sukeyi yana daga cikin aikinsu wanda doka ta basu a sashi 88 da 89 na na littafin doka na kasa ta 1999.

DOWNLOAD MP3

A yanayin raguwa ta kudin mai a Najeriya, masu fallasa sun bayyana zargin kudade da kasar Najeriya ta rasa kimanin dala biliyan biyu.
Wanda an samu wajen siyar da gangan mai miliyan 40 wa kasar China.

Gbajiabiamila ya nuna cewa Ana rasa kudade dala miliyan dari bakwai kowani wata, daga janairu zuwa yuli ta shekaran 2022 an rasa kudade har dala biliyan goma.

Shawarar kwamitin shi zai taimaka wajen yanke hukunci kan lamarin masu fallasa.
Yace masu fallasa zasu samu kariya daga majalisan tarayya.

DOWNLOAD ZIP

Kwamitin sun gayyace Ministan kudade da lauyan kasa na tarayya, Da Akanta janar na kasa da sauransu dan amsa tambayoyi.

Shugaban kwamitin, Mark Gbillah yace Suna duba da zargin gangan mai miliyan 40 da aka siyarwa China. Kuma ya kara da cewa beh ga mutunci ba dan rashin zuwan ministan kudade da lauya janar na kasa sukayi wa gayyatarsu. Duk da sun kai musu takardar gayyata.

Daga Gbillah, Yace sun samu bayani daga ofishin akanta janar cewa ministan kudade Tana saka hannu wajen fitan kudin masu fallasa wanda ya babanta da dokan.

Kuma Ana zargin akanta janar da karban kudade daga kasar waje Kuma ba saka su a asusun gwamnati a yanda dokar kasa ta tsara.

Duk yanda abubuwan suke faruwa na lamarin kudaden ba a yinsu ta yanda dace da Kuma bin doka cewar Gbillah.

Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa, NIA, Oriental Energy da CCB (code of conduct bureau) ne kadai ku amsa gayyata suka jeh gaban majalisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button