Labaran Yau

Zababbun Masu Mukaman Siyasa Na Jihar Neja Suna Kuka Saboda Rashin…

Zababbun Mukaman siyasa na jihar Neja Suna kuka rashin Albashi

Zababbun yan siyasa da aka basu mukamai a jihar Neja Suna kuka game da rashin Albashi da aka hanasu na watan maris daga gwamnatin jiha.

Dailynigeria ta rawaito cewa yan siyasan da abin ya shafa sun hada da kodinetoci, SSA, da Kuma SA.

An samu tabbacin cewa ma’aikatan gwamnatin jiha sun samu Albashin watan maris a kurarren lokaci.

Wasu zababbun masu mukaman siyasa sunyi magana da dailynigeria da kukan rashin hanasu Albashi Duk da Ana watan ramadana gwamnati bata duba musu dan su samu abun matsarufi ba.

A cewar wani dan siyasan, “Muna Azumi 21 na watan ramadan kuma kwana shabiyu cikin watan Aprailu a hakan ba a biya mu Albashi ba, tayaya ake so mu rayu?” Daya daga cikinsu yake tambaya.

Daga cikin yan siyasan Suna zargin kwamishinan kudade, Usman Muhammed, wanda yaki yabin umurnin gwamna na ya biya Albashi.

Wani wanda yaki ya bayyana kansa Yace rashin biyan Albashin da wuri ya danganci yawan bashin da jihar take ciki.

Gwamna ya bada umurnin a biya Albashi da ake bin gwamnati bashi, amma hakan yasa ya biya manyan masu mukaman gwamnati aka bar sauran.

Anyi hira da kwamishinan kudade, wanda yake cewa Duk wanda Yace ba a biyashi ba, ya fadi meyasa.

In Kuma Ana bukatan karin bayani yacewa daily Nigeria su zo ofishinsa a garin minna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button