Labaran Yau

PDP Zata Iya Faduwa Zabe 2023- Ramalan Yero

PDP Zata Iya Faduwa Zabe 2023- Ramalan Yero

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP mai adawa da su hada kansu a waje guda don ganin jam’iyyar ta samu nasara a zabukkan shekarar 2023.

Ramalan Yero ya yi kiran ne a yau Lahadi a hirarsa da kamfanin dallancin labarai na Nijeriya a Kaduna, inda ya bayyana cewa, PDP za ta iya faduwa zabe idan har ‘ya’yanta ba su hada kansu ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

A cewarsa; Idan mu ka ci gaba da fada da juna, zamu iya faduwa a zabe.

Ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ‘ya’yan PDP za su zage damtse don ceto kasar nan daga halin da take ciki, ya kara da cewa, dole ne mu ajiye son rai a gefe guda domin yin dubi kan ra’ayin ko wanne dan Nijeriya da kuma na PDP.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button