Jim kadan kafin Yan Nigeria Su Fara gudanar da zanga zangar lumana Shugaban Kasa Bola Tinubu yafitar da Manufofinsa Guda 8 Ga Yan Nigeria
Shugaban ƙasar Nageriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fidda manufofi ko ƙudirori guda 8 waɗanda ya ke son cimmawa a gwamnatinsa.
Tinubu ya gwada rashin amincewarsa na fitowa zanga zangar yanda yake bawa talakawa hakuri akan cewa sauqi nanan zuwa.
Ganin cewa mutane dayawa basusan menene kudirorinsa ba shine yasake fitowa yayi jawabi dalla dalla yanda yakeson kawo chanji a Najeriya.
Manufofin guda takwas, ga su nan kamar haka:
1. Wadata ƙasa da Abinci (Food Security).
2. Kawo ƙarshen Talauci (Ending Poverty).
3. Samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi (Eonomic Growth and Job Creation).
4. Bawa ƴan ƙasa damar samun jarin dogaro da kai (Access To Capital).
5. Kyautata tsaron ƙasa (Improving Security).
6. Kyautata sha’anin kasuwanci (Improving The Playing Field on which people and particularly companies operate).
7. Tabbatar da bin doka da ƙa’ida (Rule of Law).
8. Yaƙi da rashawa da cin-hanci (Fighting Corruption).ya Allah katabbatar dahakan Alfarman Annabi da Alkur,Ani Ameen yahaiyu yaqaiyimu.
Manufofin Tinubu kenan ga yan Najeriya.
Lallai a yanda Shugaban Kasa yayi bayani alama ya gwada cewa yayi niyan kawo sauyi a Najeriya.
Najeriya tana wani hali wanda har yakai mutane suke yunkurin yin zanga zanga saboda tsadar rayuwa.
Muna fatan Allah yakawo mana mafitar wannan tsanani da ake ciki yasa farashin komai ya sauka yanda talaka zai iya cin abinci.