Labaran YauNEWSTrending Updates

TIRKASHI: Matasa Sun Fara Zanga-Zanga A Jihar Neja – “Dole Ne Tallafin Ya Dawo”

An fara zanga-zangar wahala a Jihar Neja

Duk da rokon da gwamnati ta yi na dakatar da zanga-zanga, wasu matasa a jihar Neja sun fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne a ranar Litinin din da ta gabata, suna rera taken nuna adawa da gwamnati tare da dauke da alluna masu dauke da sakonni kamar “Ya isa haka,” “Dakatar da Manufofin Yaki da Jama’a,” “Mu Ba Bayi A Kasarmu Ba”, “Wahala Ba Ya Daurewa,” da kuma “Fuel. Dole ne Tallafin ya dawo.”

A makon da ya gabata ne Gwamna Mohammed Bago ya yi yunkurin hana zanga-zangar ta hanyar bayar da tallafin jin dadin jama’a da suka hada da alawus alawus na Naira 20,000 ga ma’aikatan gwamnati na Jihohi da na kananan hukumomi da kuma sakin metric ton 50,000 na hatsi iri-iri a farashi mai rahusa don rage radadin tattalin arziki.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button