Labaran Yau

Gwamnatin Legas Ta Yi Iyaka Wa Mutane Dan Kaddamar Da Kampanin Matatar Man Dangote

Gwamnatin legas ta yi iyaka wa mutane dan kaddamar da kampanin matatar man Dangote

Ranan Talata, gwamnatin legas ta bada shawara wa mutane suyi shirin zirga zirga ta hanyar Lekki zuwa Epe corridor kamin bikin kaddamar da kampanin matatar man Dangote wanda Shugaban kasa Muhammadu buhari zai yi ran 22 ga watan mayu.

Kwamishinan safara Dakta frederic oladeinde, ya bayyana hakan wa mutane a garin Ikeja, cewa su shirya safara da zirga zirga ta hanyar Lekki-Epe corridor tsakanin karfe 8 na safe zuwa karfe biyu na rana.

Ya bayyana cewa shawaran ya zama dole saboda kar a samu go slow a yayin tafiya saboda manyan mototi zasuyi zirga zirga a hanyar saboda bikin kaddamar wan.

Oladeinde ya jaddada cewa Hukumar kula da zirga zirgan hanya Traffic, an sanya su a hanyan dan kula da zirga zirgan hanyan dan kau da matsalolin da zasu iya aukuwa.

Yana kira ga masu mototi da sauran masu amfani da titin da su bada hadin kai wa gwamnatin jihar dan a samu a gudanar da aikin sarrafa hanyar titin cikin sauki.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button