Labaran Yau

An Kame Wani Mutum Da Ake Zargin Ya Kashe Mahaifiyarsa

An Kame Wani Mutum Da Ake Zargin Ya Kashe Mahaifiyarsa

Wani matashi dan shekara 32 da ake zargi da shan miyagun kwayoyi, Samson Sikiru, ya shake mahaifiyarsa. Wakilan mu na Labaranyau sun tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a gidan marigayiyar da ke Itanrin, Ijebu-Ode, jihar Ogun.

An samu labarin ne daga wurin dan uwan wanda ake zargin, mai gadin dare, ya sanar da makwabta game da caukuwar lamarin djim kadan bayan dawowar sa daga aiki.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, an kama Sikiru ne bayan da makwabta suka gano cewa shi ne ya kashe mahaifiyarsa, daga bisani kuma suka mika shi ga ‘yan sanda.

Majiyar ta ce wanda ake zargin ya kasance sanannen mai shan miyagun kwayoyi ne wanda ya gudu daga gida tsawon shekaru biyar kafin ya dawo kwanan nan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Omotola Odutola, ya ce rundunar ta sani.

Ta ce, “Wanda ake zargin ya kasance tare da mahaifiyarsa da ya ziyarta yayin bikin Sallah. Ko da yake an san shi da halin shaye shayen tun a baya, ana kula da lafiyarsa a sanin mahaifiyar tasa.

An Kame Wani Mutum Da Ake Zargin Ya Kashe Mahaifiyarsa
An Kame Wani Mutum Da Ake Zargin Ya Kashe Mahaifiyarsa

“Har yanzu ba a bayyana ko akwai wani abu da mahaifiyar tasa ta yi masa ba wanda ya ke ganin ta masa laifi, amma bincike na farko ya nuna cewa tun a wannan rana, an daure shi a gidan, sai kawai ya kwance kansa, ya sauka kan mahaifiyarsa, ya shake ta.”

“An ga gawar a kan gado lokacin da DPO, SP Murphy ya isa wurin. Idan aka lura da kyau, an gano alamun tashin hankali a kan marigayin.

“Lace da aka gano a kusa da kafafunta na dama ya tabbatar da cewa anyi amfani da karfi kuma akwai tashin hankali da ta shiga kafin cikawar tata.

“Samson Sikiru har yanzu yana hannun ‘yan sanda, amma babu wani abu da aka zabo daga gare shi saboda bai amsa wasu tambayoyi da aka yi masa ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button