Hukumar hajji ta kasa zata kara dala dari uku kan kudin hajji
Bincike da daily Nigeria ta yi, ya bayyana cewa Hukumar hajji ta kasar Najeriya, zata kara kudi kan kudin tafiya hajjin bana. Hakan yanada alaqa da yakin da akeyi na kasar Sudan.
Dala dari uku wanda ya kai dubu dari da talatin da tara, bayan kukan da yan Najeriya keyi kan kudi Miliyan uku na tafiya wanda Hukumar ta saka dan aikin hajjin 2023.
An samu bayanin a majiya mai karfi cewa Hukumar da jiragen sama hudu sunyi zama da saka hannu kan yarjejeniyan karin dala dari biyu da hamsin ranan talata.
Ranan Alhamis da ta gabata, Jiragen Max Air, Air Peace, Azman Air, da Aero contractor sunki su saka hannu kan yarjejeniyar saboda yakin Sudan ta kawo kulle filin jirgin su wanda hakan ya kara lokacin tashi da awa biyu.
Jami’in Hukumar hajji yace kudi dala dari biyu da hamsin zai shiga aljihun jiragen da zasuyi jigilar tafiyan ne, wanda dala hamsin zai shigo wa Hukumar dan karin da saudi tayi wanda basu saka ba lokacin fidda kudin tafiya hajjin.
Bincike ta nuna cewa Hukumar zata rubuta wa Shugaban kasa kan lamarin karin kudin tafiyan, Kamin su bayyana wa jama’a.
Jami’in hukumar ya bayyana cewa Hukumar Tana kokari ta ga ko gwamnati zata biya kudin da za biya na karin da aka samu, wanda ya kai Miliyan dala 22.5. Hakan zai dawo da shekarun da ta gabata irin yadda gwamnatin tarayya ke biyan kudaden hajji wa mutane.
Dan karin kudaden zai sa mahajjata zasu biya naira miliyan Uku da dubu dari da talatin da tara, wanda suke kudu ta Yamma zasu biya Miliyan uku da dubu dari uku da talatin da tara.
Karin baiyi wa wasu Dadi ba, amma Hukumar Tana kokari dan kar wani ya kara komai Sai dai a nemi taimakon gwamnati dan ta kara.
Daily Nigeria ta rawaito