Bazamu Zura Idanu Mu Bar Najeriya Ta Lalace Ba – Cewar Alkalin Alkalai Ariwoola
Babban Alkalin Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, a jiya, ya bukaci masana shari’a da kwararrun shari’a da kada su zauna su kalli yadda kasar nan ke tabarbarewa, sai dai su farka kan rawar da suke takawa na tsara hanyoyin ci gaban kasa.
Ariwoola, wanda ya bayyana hakan, a lokacin da yake bude taron kungiyar lauyoyin Najeriya na shekarar 2023- Sashe kan Ayyukan Shari’a (NBA-SLP), ya bukaci lauyoyin da su rungumi gaskiya, da rikon amana, yana mai cewa dole ne su bambanta kansu kuma kada su ji tsoron fafutukar ganin an yi dai dai, sus aka al`umma da kasa kawai a gaban su.
Hakazalika, a nasa jawabin, shugaban hukumar ta NBA, Yakubu Maikyau, ya ce za a kaddamar da sabuwar ka’ida ta masu aikin shari’a a ranar 1 ga watan Janairu, 2024, domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin Lauyan.
Da yake kira ga manyan lauyoyi da su bawa abokan aikinsu shawara, ya ce: “Zalunci ne ga babban mai ba da shawara kada ya bari yara kanana su sami damar zuwa wurinsu saboda ya kamata su zama masu ba da shawara. Idan ƙananan lauyoyi ba su gan ku ba, ta yaya za a yi musu jagora?”
A jawabinsa na maraba, shugaban kwamitin tsare-tsare na taron, Paul Harris Ogbole, ya bukaci lauyoyi da su yi amfani da damar taron, su kara zurfafa iliminsu na dunkulewar duniya wajen bin doka da oda. Ya ce akwai damammaki iri-iri ga lauyoyi a fagen duniya, wadanda za a gabatar da su a wurin taron.
A cikin jawabin maraba, shugaban NBA-SLP, Cif Ferdinand Orbih, ya lura cewa shekarun ilimin wucin gadi ya fadada a fannin shari’a, kuma ya kamata lauyoyi suyi amfani da shi ta hanyar da ta dace.
Ya kara da cewa taken, ‘Aikin Shari’a-Ba tare da Iyakoki ba, an zabi shi ne don adalci ga al’amuran duniya da kawo sauyi a fannin shari’a.