Yadda Ake Miyar Kubewa Cikin Minti Goma
Mutane da dama suna shan miyar kubewa don dadinta ne ba tare da sani amfanin ta ba yawan cin kubewa na daidaita gudun jini a jikin dan adam yana kunshe da wasu muhimman sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar dan adam kamarsu vitamin A, vitamin B, vitamin C da sauransu ana amfani da kubewa wajen gyaran jiki yana sa jiki tsantsi, laushi tare da sheki bari de mu koma kan girki kubewa de ya hadu.
Abubuwan da ake bukata
Kubewa
Manja
Tattasai da attaruhu
Albasa
Nama
Daddawa
Bushasshen kifi ko crayfish
Citta
Tafarnuwa
Sinadaran dandano
Yanda ake hadawa
Zaki wanke kubewarki tsafi ki tsane ta saiki yayyanka su ki daka a turmi ki kwashe a roba
Sa’annan a soya manja da albasa a zuba markadadden attaruhu da tattasai,nama,daddawa,citta da tafarnuwa a soyasu sai a zuba zuba ruwan sanwan miyan daidai yanda ake bukata a dauko bushasshen kifi a wanke da ruwan zafi a gyara a tabbatar an cire duk wasu kaya a zuba a daka crayfish a zuba da sinadaran dandano a rufe tukunyar abar kayan hadin su dafu
Bayan komi ya dafu miya ya yada kanshi sai a dakko dakakkiyar kubewar a zuba ana dan jujjuyawa kar ya dunkule sai a rufe tukunyar abar kubewar ta dafu miyar kubewa ta kammala
Sai a tuka tuwon shinkafa ko na gari ya danganta da wanda ake bukata
Ga yanda Ummi tayi nata bayanin kan yanda ake hada miyan kubewa ⇓
Yadda ake miyar kubewa me ogbono da shuwaka
Wannan miya ne da yakamata mu na yawan cinsa saboda ya tara abubuwa dayawa da jikin dan Adam ke nema kubewa de munsan wani kayan lambu ne dake da amfani sosai ga lafiya yana kunshe da sinadarai da dama haka ogbono da kubewan suma suna daidaita level din sugar a jikin mutum ga masu son rage kiba ma na temaka wajen Kona kitse ga kuma wanke ciki amfanin de suna da yawa
Abubuwan da ake bukata
Kubewa
Ogbono
Shuwaka
Manja
Attaruhu da tattasai
Albasa
Daddawa
Citta da tafarnuwa
Nama
Bushasshen kifi ko crayfish
Kayan kamshi da sinadaran dandano
Yanda zaki hada
Zaki wanke kubewarki tsafi ki tsane ta saiki yayyanka su ki daka a turmi ki kwashe a roba sai ogbono zaki hada shi da crayfish kikai a niko shi idan kina da blender kuma zaki iya nika shi a gida sai shuwakan ki gyarashi ki wankeshi dakyau zaki wankeshi ne iyakan yanda kokeson dacin ya fito a miyar
Sa’annan ki soya manja da albasa sai ki dakko nikakken ogbono da crayfish dinki ki sai ki debi soyayyen manjan kadan ki zuba akai kidan kwaba shi sai ki ajiye a gefe wannan anayi ne saboda kar ogbonan ya dunkule a cikin miyan anaso komi yayi daidai
Sai a daura nama a wuta asa citta da tafarnuwa,albasa, sinadaran dandano da kayan kamshi idan yadau dahuwa sai ki wanke bushasshen kifi ki wankeshi da ruwan zafi ki gyara a tabbatar an cire duk wasu kaya sai ki zuba su dafu tare bayan sun dafu saiki sauke
Sa’annan ki zuba markadadden attaruhu da tattasai da daddawa a sauran manjan da kika soya aka debi na kwaba ogbono idan attaruhu da tattasan sun soyu saiki juye nama da kifin da kika dafa tare da ruwan naman sai kisa ruwan sanwan miyan daidai yawanda kikeso ki rufe tukunyar
Idan miyar ya tafarfasa saiki zuba kubewar kina dan jujjuyawa da ogbonon tareda shuwakar ki rufe tukunyar abar komi ya dafu
Miya ta kammala sai a tuka tuwon shinkafa ko na gari ya danganta da wanda ake bukata