Labaran YauNEWS

Kisan Fatima Da Yaranta: Muna Kan Binciken Bidiyon Don Sanin Sahihancinsa, Cewar Buhari

Kisan Fatima Da Yaranta Muna Kan Binciken Bidiyon Don Sanin Sahihancinsa Cewar Buhari

Yanzu haka fadar shugaban kasa (Villa) ta gargadi yan Najeriya kan yunkurin mayar da martani bisa bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta na kisan wata mata ‘yar Arewa wanda takeda juna biyu tare da ‘yayanta hudu.

Wanda yake magana da yawun shugaban kasa, mai suna Malam Garba Shehu, a jawabinsa da ya fitar ranar Laraba yace Shugaba Buhari ya kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin kan bidiyon.

Ya ce masana na kan gudanar da bincike kan bidiyon don sanin ko gaskiya ne ko ba gaskiya bane.

DOWNLOAD MP3

A cewar jawabin:

“Fadar shugaban kasa na gargadi kan yunkurin tada tarzoma, lalata dukiya ko mayar da martani kan bidiyon da ake zargin yan kungiyar Eastern Security Network (ESN) da kashe yan ci rani.”

“Yayinda masana ke gudanar da bincike kan gaskiyar bidiyon, muna kira ga yan Najeriya kada suyi gaggawan hukuncin da ka iya tada tarzoma.”

DOWNLOAD ZIP

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da kashe-kashe mutane da akeyi a yankin kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya.

Shikenan Ba Ni Da Kowa Cewar Mijin Da Aka Kashe Mata Mata Da Yara 4 A Anambra

Mijin mata mai ciki da ‘ya’yanta hudu da ‘yan IPOB suka kashe, mai suna Jubril Ahmed, yafito yayi jawabi yayinda ya ce har yanzu yana cikin rudani da tashin hankali,Jubril da ke aiki a matsayin mai gadi a jihar Anambra ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa matarsa tana gab da haihuwa a lokacin da abin ya faru.
Ya ce,

Domin Samun Isashen Labarai Ka Cigaba Da Shigowa Shafin Jaridarmu Ta Labaranyau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button