Hadakaiyar Arewa ta tsakiya sun hadu dan goya wa Gagdi baya na zama shugaban Majalisan tarayya
Hadakayyar gudanarda mulki na cigaba ta Arewa ta tsakiya (NCCGG) sun bayyana cewa dan majalisa mai wakiltar Pankshin, Kanke, Kanam a yankin jihar filato, Yusuf Gagdi, shi yafi cancanta da shugabancin kakakin majalisan taryayya, a majalisa ta goma.
Wanda ya jagoranci hadakaiyar, Abraham Dauda, ya bayyana wa manema labarai a Abuja jiya, cewa sunyi shawara da magabata da mutane.
A cewarsa Gagdi mutum ne jajircacce, meh hazaka, zafin nama, da Kuma san cigaba a kowani lokaci, Kuma abinda yayi a baya na aiki da kishi ya nuna hakan.
Dailytrust ta rawaito cewa Dauda, yana bada shawara wa Jam’iyar APC da wasu jiga jigen sauran yankin dasu kawo shugabancin majalisa zuwa Arewa ta tsakiya. Kuma su bada Gagdi dama dan cancantar sa.
Ya kara da cewa suna mika kokon baransu wa jam’iyar APC da ta bada Arewa ta tsakiya dama dan fitar da shugaba a majalisan ta goma. Kuma Suna neman Duk sauran jam’iyun da su bada dama wa Arewa ta tsakiya dan cimma burin hakan.
Yace, “shi Gagdi mutum ne wanda yasamu wayewar kai akan abubuwan da ta shafi kasa gaba daya, Kuma yayi abinda ya kamata a matsayinsa wanda ya shafi kawo cigaba wanda Duk shugaba nagari yakamata yayi dan bunkasuwar cigaba a kasa”.