Labaran Yau

Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Wanda ke Shiga Gonakin Mutane A Jihar Filato

Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Wanda ke Shiga Gonakin Mutane A Jihar Filato

Sojin kasa mai taken Operation Safe Haven, wanda ke kula da tsaro dan samun zaman lafiya a Jihar Filato da kewaye ta kama shanu da tumakai 1000 wanda ke kiwo a gonakin mutane a karamar hukumar Mangu na jihar Filato.

Kaptin James Oya, jami’i mai kula da shafin Sadarwa na Sojin, ya bayyana hakan ranan laraba a Jos.

“A kokarin da mukeyi dan magance matsalar tsaro a Mangu, sojoji na Operation Safe Haven sun kamo shanu da tumakai guda 1000 wanda ke kiwo a gonakin mutane a wani kauye mai suna Dumunan a garin Bwai a karamar hukumar Mangu.

Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Wanda ke Shiga Gonakin Mutane A Jihar Filato 
Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Wanda ke Shiga Gonakin Mutane A Jihar Filato

“Bincike ta nuna cewa shanun da tumakan sun fito daga karamar hukumar Bokkos da barikin Ladi.

“Wannan dabbobin Suna hanun mu dan daukan matakin da ya dace”.

Shi sojin Mista Oya bai bayyana ko masu dabbobin da aka kama su ma an kama su ba.

Jami’in Shafin safarwan ya nuna shirin da Kwamanda na Operation Safe Haven, Major Janar Abdusalam Abubakar yayi dan kawo katshen kai farmaki da kashe kashe a Mangu da kewaye.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button