Labaran Yau

Yan Fursuna 3 Sun Kammala Karatun Digiri

Yan Fursuna 3 Sun Kammala Karatun Digiri

Yan Fursuna uku na Gidan fursun da gyaran hali na Kuje, sun kammala karatun su na Digiri da diploma a fanni daban daban a jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN).

An bawa Yan Fursunan takardan shaidar karatun a bikin gama karatu da jami’ar NOUN ta shirya a cikin gidan fursun da ke garin kuje na Abuja.

A cikin su Yan Fursunan akwai Dabu Christian Picador wanda ya kammala digiri A Harkan kasuwanci da gudanar da kasuwa (Bsc Entrepreneurship and Business Management), Akwai Nurudeen Na’Allah wanda shi ma ya kammala digiri a kan karatun Firamare (B.Ed Primary Education), Sai Jacob Olom wanda yayi karatun sama da digiri a fannin kasuwanci (PGD Business Administration).

DOWNLOAD MP3

A bayanin kwantrola janar na gidan gyaran hali na kasa Haliru Nababa, yace hakan ya nuna hanyoyi da yan fursuna zasu rinka bi domin tsara rayuwarsu su zama mutane na kwarai masu amfani a cikin mutane bayan sun fito daga fursuna.

Ya ce ilimi itace babban mafita ma mutane da gari ba ki daya. Ya gargadi Yan Fursuna da suyi amfani da wannan daman na karatu wanda hadin kai na NCoS da NOUN suka kawo dan samun takardu.

Nababa ya samu wakilci daga shugaban ofishin su na Abuja Ibrahim Idris yace su Yan Fursuna guda ukun sun daga kan su dalilin karatu, sun cire tsoro Kuma babu mai rainasu Duk inda suka sami kansu.

DOWNLOAD ZIP

Ya Kuma yabawa Jami’ar NOUN wajen goyon bayan gyara Yan Fursuna ta hanyar bada ilimi, yace tun bayan hadakaiyar, sama da mutum 200 Yan Fursuna sun koma karatu daga fursunan kuje kawai.

Nababa ya bada shawara wa Yan Fursuna da su yi amfani da daman da suka samu na karatu da koyon aikin hanu kyauta. Dan su maida kansu masu karatu da sana’ar hanu domin samun jin dadin rayuwa.

Shugaban Jami’ar NOUN Farfesa Olufemi Peters ya taya su murna bayan kammala karatu. Yace hakan ya nuna jajircewansu wajen gyara rayuwar su.

Modupe Adesina wanda ta wakilci mista Peters ta ce, Duk da irin halin da suke ciki, karatun zai taimaka musu wajen zama wasu a cikin Al’umma.

Shugaban NOUN yace suyi amfani da damar suyi karatu wajen inganta rayuwarsu da Kuma dogaro da kai in sun fita a gidan gyara hali.

Daraktan wajen karatun yan fursuna, Francis Enobore yayi kira ga mutane da su daina nuna su dan sun taba laifi, yakamata a mara musu baya ne dan inganta rayuwarsu dan su zama mutane nagari.

Mataimakin shugaban gidan gyara hali na kuje Christopher Jen, ya yaba musu wajen kammala karatu Kuma ya basu shawarar koyon sana’ar hanu dan samun abun yi bayan an sake su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button