Police Command na Borno ta bayyana cewa an samu asarar rayuka biyu yayin da jami’anta suka dakile wani hari da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai a barikin ‘yan sanda na Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Nahun Daso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri ranar Lahadi, ya ce an kai harin ne da sanyin safiyar Lahadi.
A cewarsa, daukin gaggawar da jami’an rundunar ‘yan sandan tafi da gidanka da ke ofishin ‘yan sanda na Jakana suka yi, ya fatattaki maharan, tare da hana su mamaye kadarorin ‘yan sandan.
Bayanan ASP Daso A Churewar ‘Yan sanda da Boko Haram
ASP Daso ya bayyana cewa an yi asarar rayuka guda biyu a musayar wuta da aka yi, ga bayanan shi dalla dallah:
“An yi asarar rayuka guda biyu. Sun hada da dan sanda da wata farar hula. Bugu da kari, an kona motar ‘yan sandan da ke sintiri a yayin da lamarin ya faru.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Borno, CP Yusufu Lawal, ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da tabbatar da cewa an fara gudanar da bincike mai zurfi.
“An kuma dauki matakan tsaro don hana kai hare-hare,” in ji shi.