Labaran Yau

Yunwa Ta Shafi Mutum Miliyan 4.3 a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Yunwa Ta Shafi Mutum Miliyan 4.3 a Arewa Maso Gabashin Najeriya Cewar Jami'in Majalisan Dinkin Duniya

 

Jami’in jin kai na Majalisan dinkin duniya a Najeriya Mathais Schmale, yace yunwa matuka yana damun mutane a kalla miliyan 4.3 a Najeriya ta yankin Borno, Adamawa, da yobe.

Mista Schmale ya fada wa yan jarida a Geneva ranan laraba cewa adadin yara da rayuwansu keh cikin hatsari ya nika so biyu ya kai dubu dari bakwai.

Bayani akan lamarin ta Arewa maso gabashin Najeriya, Mista Schmale yace “ naje Borno da jihohi guda biyu lokuta daban daban.

“Naga iyaye mata Suna yaki dan ceto rayuwar yaransu wanda basu samu isheshshen abinci.

“Mu da muke iyaye dole muyi tunanin yanda yara zasu kasance in babu abincin da zasu ci”. Cewar sa.

A bayanin shi ya nuna cewa matsalar yunwa Tana daga cikin abubuwa da suka taimaka wajen karuwar rashin tsaro da aka fuskanta fiye da shekaru goma da ta gabata. Hakan ya hana noma da neman arziki domin magance matsalar yunwa.

Wata matsalar ta allaka da yanayin zafi  da Kuma  canji na ruwan sama a wannan yanki.

Shekarar da ta gabata ta ga ambaliya da yafi na shekaru goma da suka wuce wanda ya shafi mutum sama da miliyan 4.4 a kasar, ba Arewa maso gabaci ba kawai.

Hawan farashin kayan abinci, man fetur da taki ya taimaka wajen lamarin wahala. Kuma taimakon ya kasa wanda ake yi.

Jami’in Majalisan dinkin duniya yace cikin dala biliyan 1.3 na jin kai wa yankin. Kashi 25 cikin dari na kudaden aka samu a Yanzu haka.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button