Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya raba riyal 300 wa Duk mahajjaci wanda sun fi mutum 3000 na Bauchi a kasa mai tsarki na Makkah.
Hakan ya fito cikin jawabin da mai bada shawara Alhaji Mukhtar Gidado yayi ranan jumma’a a Bauchi.
Gidado yace gwamnan yayi kyautar yayin da yaje masaukin Alhazai na kasa Mai tsarki dan tattauna wa dasu.
Hukumar labarai ta kasa ta bada rahoton cewa riyal 300 yanada kimanin Naira 75000.
Gidado yace gwamna yayi hakan ne dan tallafa wa mahajjata wajen kawo sauki a yayin zaman su a saudiyya.
Gwamnan yace bayan ya ziyarce masaukin mahajjatan ya yaba musu wajen kiyaye dokoki a saudiyya.
“Mohammed ya yaba musu wajen girma jami’ai a gida Najeriya da waje kasar saudiyya.
“Ya jaddada cewa gwamnatin shi baratayi kasa a gwiwa wajen taimako wa mahajjata a jihar shi da Hukumar don samun ingancin gudanar wa na mahajjata” a cewar sa.
Gidado ya kara da cewa gwamnatin jiha zata hada kai da Hukumar Alhazai ta kasa wajen kawo maslaha kan kalubalen da Hukumar Alhazai ta jiha ke fuskanta a kasa mai tsarki.
Ya ce gwamnan ya nuna godiyansa a bayyane wa mahajjata dan adduoi da sukayi masa da mulkinsa na cigaba a kowani lamura, kuma ya bada shawaran a ciga da hakan.