Labaran Yau

DAGA SUDAN: ‘Yan Nageriya Mafiya Yawansu ‘Yan Arewa Suna Cikin Bala’i Direbobin Mota Sun Ajiyesu

DAGA SUDAN: ‘Yan Nageriya mafiya Yawansu ‘Yan Arewa suna Cikin Bala’i direbobin mota sun ajiyesu a tsakiyar daji sunce ba zasu matsa ba sai Gwamnatin Nageriya ta biya su ku’din su.

Lallai mutanenmu yan Najeriya da suke Sudan suna cikin wani mawiyacin hali

Ga Sakon da daya daga cikin dalilan Ya turo ma Jami’inmu na Labaranyau yanzu.. 👇

Muna waya da daya daga cikin yan uwa da aka sauke a dokan daji cikin sahara, Babban abinda yafi daga min hankali shine kukan jarirai, sakamakon babu Ruwa ballantana abinci, yunwa da ƙishi da zafin Rana ya damesu. Bazasu iya dawowa Khartoum ba, sannan babu halin karawa gaba. Su kuma direbobi sun ce Bazasu ci gaba da tafiya ba har sai an biya su kuɗin su complete. ( Wanda a farko an sanar mana cewa an biya kuɗin motoci 40 da zasu kwashe mu zuwa cairo).

Mu kuma da muke cikin Khartoum muna jira yau motoci 27 suzo su kwashe mu saboda mu tsira da ranmu, Har yanzu babu mota kwaya daya da tazo, Ga fargaba dangane da karar bindigogi da tashin bama-bamai.

Da gilmawan jiragen yaƙi! Banda kuma zafin Rana da yunwa da ƙishi.

Babban wurin da akayi sansani domin jiran motocin wato ( IUA) shi kan shi akwai hadari a zaman Wurin, ka cire maganar Rashin ruwa da Rashin abinci, wuta ta dauke a Wurin.

Yana kusa da ɗaya daga cikin manyan sansanonin RSF , wanda a ko wani lokaci sojojin gwamnati zata iya kawoma wurin farmaki.

Jiya kwana akayi a Unguwarmu ana bata kashi, tsakanin bangarorin biyu.. haka muka kwana , sannan muka wayi gari da Hakan.

Hakan na zuwa ne fa duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin kwanakin. To da babu yarjejeniyar mai zai faru kenan?

Muna Rokon yan uwa su tayamu da addu’a Allah ya karkato da Hankalin waɗanda abin ya shafa, su gane wannan abinda sukeyi wasa suke da Rayuwar Al’ummah.

Ran dan adam yana da tsada!

Gwamnatin tarayya ta amince a fitar da kudi dala miliyan 1.2 dan fitar da yan Najeriya

Ministan kula da Al’amuran waje, Goeffrey Onyeama, ya bayyana sakamakon zaman da sukayi wa manema labarai, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman ranan laraba a Birnin tarayya Abuja.

A cewar Onyema, kudaden za kashe su ne wajen hayan manyan mototi dan safaran yan Najeriya a Sudan zuwa Kasar masar inda jirgi zata kashesu zuwa Najeriya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button