A yayin zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Audu ya tabbatar da aniyarsa ta dawo da masana’antar karafa da ta lalace.
A cewarsa, zai tsara taswirar ci gaban harkar karafa, da yin zage-zage wajen kammala aikin karafa na Ajaokuta, da kuma samar da kudirin doka da ake bukata domin daidaita bangaren karafa da dai sauransu.
Ya ce, “Shugabannin mu na baya sun fahimci mahimmancin bunkasa karafa amma ba su da kishin siyasa don cimma manufofin sa.
“Haɓaka karafa yana daidai da kamfanin Ajaokuta Karfe, wanda aka fara shi sama da shekaru 40 da suka gabata. Muna da burin yin aikin tare da tabbatar da cewa mun samar da aƙalla sarrafa karafa a cikin wannan gwamnati.
“ Sanin kowa ne cewa karfe shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa; idan aka yi daidai, to yana iya zama farkon juyin juya halin masana’antu.”