Labaran Yau

Majalisan Tarayya: Meyasa Matatan Man Najeriya Basu Aiki Bayan Kashe Naira Tiriliyon 11

Majalisan tarayya: Meyasa Matatan man Najeriya basu aiki bayan kashe naira Tiriliyon 11

Kwamitin matatan mai na Majalisan tarayya Ta bayyana cewa an kashe Naira tiriliyan 11 dan gyarawa amma an samu akasin haka da biyan kudin aiki so biyu.

Maganar ta fito ta bakin dan Majalisa mai jagoran kwamitin Ganiyu Johnson. Ya bayyana rahoton a Majalisan tarayya a Abuja.

Yanayin da matatan man bayi motsi wajen cigaba da dawo dashi aiki tun tsakanin 2010 zuwa 2020.

Kwamitin tace matatan man kasan basu aiki, sun lalace, Kuma barasu iya kaiyade nawa za a kashe wajen gyara su ba tsakanin lokaci ba.

Sun kara bada shawaran NNPCL su yi amfani da wannan dama wajen amfani da dokar mai ta 2021. Wanda Majalisan tarayya ta kawo hakan zai taimaka wajen samun cigaban matatar.

Sun ce NNPCL da yan kwangila Tecnimont SPA na kasar Italy suyi kokari dan matatar Olone na Portharcourt ta fara aiki.

Matatar Tana iya tace gangan mai 60,000 a rana, a halin yanzu zata iya tace gangan mai 54,000 wanda zata iya aiki kashi 90 cikin dari.

Kwamitin tace aikin zata iya kammaluwa zuwa Satumba, 2023. NNPCL da yan kwangilar ya kamata su zage damtse dan karasa aikin matata 1 da 2 na sabon matatar Portharcourt.

A bayanin kwamitin hakan zai kara yawan tatan mai kimanin ganga 150,000 a rana, wanda a kalla a lalace za a iya tace 135,000 a rana.

In anyi hakan zai sa a iya tace mai ganga 189,000 a rana kuma a cimma burin disamba 2023, a shawarar da suka bayar.

Daily Nigeria ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button