Labaran Yau

Shugaban Hukumar EFCC Ya Nemi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu Inji Matawalle

Shugaban Hukumar EFCC ya nemi cin hancin Dala miliyan biyu inji Matawalle

Gwamnan jihar zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa yana fuskantar wulakanci wurin ciyaman din Hukumar Kula da laifin tattalin arziki da kudi EFCC Abdulrasheed Bawa, saboda hana shi kudin cin hanci dala biliyan biyu.

Ranan Alhamis, Hukumar ta bayyana cewa Matawalle Ana bin ciken shi da canzawa kudin jihar sama da naira biliyan saba’in wurin zama.

Amma bayan hira da BBC Hausa tayi dashi Matawalle ranan jumma’a, ya bayyana cewa shi bai saci kudin jihar ba.

“Bincike yana da kyau, ina bayan ayi. Kuma bai kamata a zabi wanda za a bincika ba, yakamata ayi shi gaskiya wajen yin komai ba zallan gwamna ba. Ba gwamnoni kawai suke iya aiwatar da aiki da kudin gwamnati ba, akwai ministoti Kuma yakamata a nemesu su a bincike su” inji shi.

Matawalle yace Bawa ya dukufar da kanshi wa bincike, saboda shima akwai zargin rashawa akanshi.

“Ina Kalubalantar shi (bawa) da ya nuna wa duniya duka takardan shaidan badakalan da yake dashi akan gwamnoni, Kuma shi ma ya mika wuya dan a bincike shi dan laifin badala da ke rataye a wuyansa.

“Sama da mutum dari biyu Suna shirye dan su shaida cewa hannun shi ya yi cikin rashawa da badakala.

“Yasan abinda ke tsakaninmu, ya nemi alfarma a wurina na hana, Sai yasa ya zabi ya ci mutunci na, amma ban damu ba.

“Duka zargin da akeyi akaina karya ce, ya nemi in bashi cin hancin dala miliyan biyu kuma na hana, Kuma ina da Shaidu.

Matawalle yace a zaman da sukayi tsakaninsu, shugaban EFCC ya tugume shi da rashin zuwa ofishin shi yadda wasu gwamnoni keyi.

Bayan BBC sun nemi shugaban Hukumar dan suji ta bakin sa, bawa ya bayyana cewa mutum Tara yake bai cika goma ba, amma yana kalubalantar Matawalle ya bayyana laifukansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button