Labaran Yau

Sojoji Sun Shirya Tsaf Don Yin Juyin Mulki A Kasar Niger Republic

Sojoji Sun Shirya Tsaf Don Yin Juyin Mulki A Kasar Niger Republic

A safiyar yau Larabar ne jami’an tsaro suka rufe kofar shiga gidan shugaban Kasar Niger Republic da ofisoshi da ke cikin fadar, kuma bayan tattaunawar da aka yi “sun ki sakin shugaban”.

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a yau Laraba da yana tsare tare da wasu jiga-jigan dakarun tsaron fadar shugaban kasar da ba`a gamsu da su ba, wanda su kuma sojojin suka ba su wa’adi domin su bar wuraren da suka tsare, kamar yadda wata majiya da ke kusa da Bazoum ta bayyana a ranar Laraba.

Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunkurin juyin mulki tare da yin kira ga “masu makirci” da su saki Bazoum nan take ba tare da wani sharadi ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

An zabi Bazoum ne a shekarar 2021, inda ya karbi ragamar mulkin kasar da ke fama da talauci da tarihin rashin zaman lafiya.

A cikin wani sako a shafin Twitter, wanda ake yiwa lakabi da X, ofishin shugaban kasar ya ce “bangaren dakarun tsaron fadar shugaban kasa (PG) sun yi fushi…

“Rundunar soji da masu tsaron kasa a shirye suke su kai farmaki kan ‘yan ta’addar PG da ke da hannu a cikin wannan yunkuri idan ba su dawo cikin hankalin su ba,” in ji fadar shugaban kasar.
“Shugaban da iyalin sa suna cikin koshin lafiya,” in ji shi.
Ba a bayyana dalilin fushin masu gadin ba.

An tare hanyar shiga harabar fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, duk da cewa babu wani sansani na sojoji ko karar harbe-harbe a yankin, kuma zirga-zirgar ababen hawa bai fasu ba, kamar yadda wani ganau ya shaida wa wakilan mu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar daga Najeriya, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaban da aka zaba ta hanyar dimokradiyya.

Kungiyar ta yi gargadin cewa, kungiyar da kasashen duniya baki daya za su rike duk wadanda ke da hannu a wannan badakala, kuma zaa tuhume su kan batun lafiyar Bazoum, da iyalansa, da na gwamnati, da kuma jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button