Labaran Yau

Kotu Ta Amince Da Kama Imam AbdulAziz Na Bauchi

Kotu ta Amince da kama Imam Abdul Aziz Na Bauchi

Malam Husaini Turaki na babban kotun Shariah a Bauchi ya sanya hanu kan takardan amincewar kama shahararren malamin addini Kuma babban limamin Masallacin jummuah na dutsen tanshi, Dakta Idris AbdulAziz dan rashin halartan gayyatan kotu.

Dayawan mutane basusan waye Dr Malam Idris Abdul Aziz Bauchi ba saida wannan abun ya faru.

Daily trust ta bada rahoton cewa An kulle Malam Idris kwanakin baya a Kurkuku dan kawo rudani tsakanin jama’a.

Limamin ya kai kwana bakwai a gidan horo, a yayin da aka karbi belin shi da naira miliyan daya. Da Kuma wanda suka tsaya masa mutum uku wanda doka ta bada ya hada da sarkin gunduma, Famanet sakatare na jihar Bauchi da kuma babban malamin Addini na jihar.

An sake limamin bayan cika sharudai na beli, Yan kasuwa guda biyu da manyan Malamai guda biyu a kotun jihar.

Yayin da aka dawo kotu jiya, shi malamin bai halarci zaman ba.

Aliyu Ibn Idris wanda ya tsaya a maimakon ministirin adalci bayan magana da yan jaridu, ya bayyana cewa an daga shariar daga kotun majistiret zuwa babban kotun shariah.

“Sun yi rubutu kan cewa basu yarda da matsayin kotun ba kan shariar, Kuma Sai bai kawo kanshi gaban kotun ba.

“Munyi magana cewa Sai ya kawo kanshi kotun, amma bayan yaki halarta Sai muka nemi kotu ta bada daman kama shi wanda kotun ta bayan” cewar Ibn Idris.

Lauyan limamin Sadiq Abubakar Ilelah, yace malam Baida lafiya ne dalilin rashin zuwa kotun kenan.

“Mun ba kotun hakuri da alkawarin kawo shi lokacin da kotu ta saka. Amma kotun ta ki amincewa da dalilin cewa limamin bai girmama kotu ba” in ji Ilelah.

An daga zaman Sai litinin mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button