Baran tsoma baki a Gwamnatin Abba ba- inji kwankwaso
Tsohon gwamnan kano, Sanata Rabiu Musa kwankwaso yace bare tsoma baki a gwamnatin gwamna meh jiran gado, Abba Yusuf ba.
Kwankwason wanda shine shugaban jam’iyyar nnpp ta kasa ya kara da cewa a matsayinsa na cikakken dan jihar zai kasance me bada kyakkyawar sharwara wa gwamnatin ne a lokacin da ta bukata
Tsohon dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar nnpp ya fadi hakan ne a wajen tattaunawarsa da BBC hausa bayan hayaniyar da wasu ‘yan Najeriya sukeyi akan bazai bar sabon gwamnan ya gabatar da tashi kudurorin ba
Amma shugaban jam’iyyar nnpp ya bayyana cewa bazai yi mubaya’a da sabon gwamnatin ba a Duk lokacin da yaga Suna kokarin kauce hanya
Ya kara da cewa ko da me goge gogen ka ne ka zaba a matsayin shugaba to kada ka mai kutse idan ya tambayeka shawara zaka bashi idan Kuma be tambayaba kayi shiru
“A lokacin da nake gwamna nayi aiki da wasu mutane cikinsu akwai abba wanda suka temakeni na cimma Nasara
“Wannan shine yasa muka zauna muka duba a gabadaya mutanen mu,Kuma muka zabi wanda muke tunani Kuma muke sa ran idan Allah ya taimaka bazai Maimaita rashin hankalin ganduje ba
“Ko ma waye yake mulkin kano ko soja ne koma waye bara mu barshi ya kauce hanya ba
“Saboda haka koda Abba ne ya yi shugabancin ko ma waye zamu fada mishi komai da yake daidai da lokacinda yake ba daidai ba Duk zamu fada mishi
“Abinda nasani shine Duk wani abin da be kamata ba a lokacin wannan gwamnati me ci zaa gyara.”
Daga Raheela Usman