Wanene Dr Imam Idris Abdul Aziz Dutsen Tanshi?
Malam mutum ne wanda ya shafe shekaru kusan talatin yana karantar da sunnar mai gidan shi kuma ma’aiki, Annabin Rahama (saw), kullum bashi da aiki sai kafa sunnar Manzon Allah (s) da yaqar mutane masu qirqiro sabbin ibadu wanda babu su cikin koyarwar Manzon Allah (s)!
Malam mutum ne wanda yabi salon da’awar Manzon Allah (s) na karantar da;-
(1) Aqeedah/tawheed.
(2)Shari’ar da sunnar Manzon Allah (s).
(3)Da kuma yaqar zalunci: Malam yayi fada da miyagun ‘yan siyasa, miyagun ‘yan gargajiya, miyagun ‘yan ta’adda da sauran miyagun qungiyoyin mutane azzalumai.
(4)Ya yaqi qungiyoyin yahudu da nasara masu farautar ruguza tarbiyyar musulunci.
Samun malamai magada Annabawa irin su Dr Idris a yanzu sai an darje!
Malam Dan Adam ne, yana da qura-qurai da gazawa a matsayin shi na mutum, amma danganta cewa maqiyin Annabi (s) wannan tsabar zalunci ne, da sharri.
Abinda Malam yace shine ba a roqon Annabi a yayin da ka shiga musiba, Allah ake kira!
Shin idan na daukaka hannuwa na biyu ina roqon Annabi (s) ya bani arziqi, ko ya bani Aljannah baza kuce na zauce ba?!!! Tou ashe kenan kun yarda ba a roqon kowa yayin musiba sai Allah!
Kuskuren Malam shine usulubin maganar, amma saqon maganar daidai ne! Kowa ya sani Annabin Rahama (s) ya koyar da duk halinda muka tsinci kan mu Allah zamu roqa ba shi ba!
Akwai haqqin Allah, akwai haqqin Annabin Rahama (s), sannan akwai haqqin Alqur’ani mai daraja!
“Ku tambayi malamai idan baku sani ba”.
Daga; HON Sulaiman shuaibu Abubakar ✍️