Labaran Yau

Ramadan 2023: Abu Meh Kamar Wuya Rashin Tashin Farashin Kayan Abinci A Jahar Katsina

Rashin tashin farashin kayan abincin a jihar katsina a watan ramadana Abu meh kamar wuya

Kwastamomi da yan kasuwa sun yaba da rashin tashin kayan abinci a watan ramadana wanda hakan keh faruwa ko wata shekara.

Kayan Abincin ya kasance yana tashi Duk lokacin da Azumin watan ramadana ya gabato, a wannan shekarar tazo da sauki ya yin da yan kasuwa basu qara farashin ba.

Menama labaran trusttv sunyi hira da mutane Kuma sun bayyana musu farin cikin su da Kuma dalilin da yasa kayan abincin beh tashi ba a wata meh tsarki ta ramadana.

Wanda ya kunshi rashin kudi a gari Yasa jama’a basu damu da siyan kayan abincin ba. Hakan ya taimaka wajen tsayawar farashin abincin waje guda.

Daga bakin wani dan kasuwa Yace mafi yawan ma aikata basu ziyarci kasuwaninsu domin siyan kayan abinci ba saboda an fara azumin watan ramadan kusa da karshen wata, Kuma ma aikata dayawa basu samu Albashi ba.

Sun hada kiret din Kwai har yanzu yana nan a dubu daya da dari takwas wanda wani dan kasuwa Yace yakan siyar da kiret ashirin amma yanzu baifi kiret goma yake siyarwa ba saboda rashin kudi a gari.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button