Labaran Yau

Makaranta Mai Dadalibai 350 Malamai 3 Kacal Suke Dashi A Jihar Bauchi

Makaranta Mai dadalibai 350 Malamai 3 kacal suke dashi a Jihar Bauchi

Al’umman Gabchyar na karamar hukumar Darazo na Jihar Bauchi, sunce Makarantar Firamare da Sakandare kananan ajujuwa zuwa JSS 3, wanda shine Makaranta guda a kauyen. Malamai Uku kacal suke fashi.

Mutanen kauyen sun bayyana hakan wa yan jaridar Hukumar labarai ta kasa a gabchyari ran litinin.

Sunce hakan ya kara yawan yaran da basu zuwa Makaranta a wannan yankin Kuma Suna mika kukansu wa gwamnatin Jihar Bauchi da su Samar musu malamai a Makarantan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Daya daga cikin shugaban kauyen Malam Isa Ibrahim, yace rashin malamai a Makarantan ya kashe karfin gwiwan Iyaye dan kai yaransu Makaranta.

“Muna so gwamnati ta taimaka mana da Malamai, malamai suna da muhimmanci Kuma Muna bukatan su a Makarantan” a cewar sa.

Mazaunin garin Yahya Adamu, yana kiran gwamnati da su kyara Makarantar dan yara su samu karatu cikin inganci da nutsuwa.

Ya bayyana cewa cikin jeren ajujuwa 6, 2 daga ciki ne kawai suke da kyau.

Adamu Yace rashin ruwan sha yana daga cikin matsalolin su wanda yake hana iyaye tura yaransu zuwa Makaranta.

“Yana da matukar wuya samun ruwa, hakan yasa yara dayawa Suna yawo neman ruwa a lokutan da yakamata Suna Makaranta.

“A dalilin haka suke gajiya in sun Isa Makaranta bayan sun makara saboda wahalan neman ruwa.” A cewar sa.

ABDULLAHI Muhammad, malamin Makaranta yace sakandare Tana da malamai 3 Kuma firamare Tana da malami 1.

“ mutane sukan tambaye mu cewa mai muke koyar da daliban kasance war mu uku ne kacal a Makarantar.

“ Muna da malami daya wanda yake aikin shugaban Firamare wanda ke da dalibai dari biyu da Kuma sakandare Mai dalibai dari da hamsin.

“Mafi yawan lokuta ni da Dayan malamin mukan taimaka wajen koyarda ajujuwan Firamare, Muna iya kokarin mu.” Inji shi.

Abdullahi Muhammad wanda shine mai magana da yawun SUBEB yace karamar hukuma ce ta ke da karfin tura malamai karkashin sakataren Ilimi.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button