Labaran YauNEWS

Shawara Mafi Muhimmanci Ga Mace Da Ke Son Daukar Ciki Ko Samun Juna-biyu

Shawara Mafi Muhimmanci Ga Mace Da Ke Son Daukar Ciki Ko Samun Juna-biyu

Babu mamaki akwai tarin tambayoyi a zuciyarki kan yadda zaki dauki ciki, musaman idan kina da larura ko wani ciwo. Kula da lafiyar jiki na cikin matakan farko na iya samun dacewar daukar ciki. Amma kuma me za ki iya yi domin inganta hanyoyin samun haihuwa?

Shawara mafi muhimmanci ga mace da ke son daukar ciki ko samun juna-biyu ita ce sanin yanayin jikinta, musamman lokacin zuwan jinin al’adarta, a cewar Dakta Sajeeda Ibrahim, ƙwararriyar likitar mata a Asibitin Koyarwa na birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

DOWNLOAD ZIP/MP3

“Yana da muhimmanci ta san yanayin zuwa da ɗaukewar jininta na haila saboda tsara ko sanin lokutan da idan ta yi jima’i za ta dauki ciki,” a cewar Dakta Sajeeda.

An tattauna da Dakta Sajeeda da kuma Dakta Tanko Zakari, kwararre kan lafiyar mata a Asibitin Mallam Aminu Kano, kan matakai bakwai da za su taimaka wa mace wajen ɗaukar ciki.

1. Bincike domin sanin yanayin lafiyar jikinki

Kafin ki soma kokarin ɗaukar ciki, ki soma duba lafiyarki. Ki tambayi likitarki domin samun bayanai kan magunguna da ke taimaka wa mace wajen ɗaukar ciki – masu dauke da sinadarin folic asid da ke taimakawa da kuma bayar da kariya kan wasu matsalolin haihuwa da suka hada da haihuwar jarirai masu nakasa.

Sinadarin folic asid na aiki sosai a kwanakin farko na ɗaukar ciki, shi ya sa yake da muhimmanci ki tabbata kina shan sa sosai tun kafin ki yi ciki.

Ki tabbatar kina bin wannan tsari kafin kokarin ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda. “Idan kina da matsala da lalura dole ki nemi magani da daidaita kanki kafin ki samu ciki ba tare da matsala ba.”

2. Sanin lokutan haila

Me kika sani game da lokacin zuwa da ɗaukewar hailarki? Fahimtar hakan zai taimaka miki wajen sanin lokacin da ya fi dacewa na daukar ciki a gare ki a cewar, Sajeeda.

Lokacin da mahaifar mace take fitar da kwayaye shi ne mafi dacewa wajen daukar juna-biyu a gare ta.

“Wannan shi ne lokacin da ake son mace ta nuna nacewa wajen jima’i a kai-a kai,” a cewar masana.

Hakan na taimakawa wajen gane alamomin fitar kwai, da sauye-sauye da mace ke ji a jikinta da fitar ruwa daga farjinta.

Ruwan na kasancewa fari da ɗan kauri da yauƙi wanda ke isar da sakon cewa shi ne lokacin iya samun juna-biyu. Wasu mata kuma kan yi fama da ciwon mara.

Sannan akwai abin da ake amfani da shi wajen gwada ko mace ta soma fitar da ƙwai wanda shi ma yana taimakawa wajen ankarar da cewa tana cikin lokacin iya ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button