Labaran YauPolitics

Wajibi Ne Ga Duk Mai Kishin Jahar Bauchi Ya Bawa Kauran Bauchi Dama Karo Na Biyu – Shu’aibu Nasiru Dass

Ga Abinda Shu’aibu Nasiru Dass Ya Fada A Gameda Zaben 2023 Dake Gabatowa Na Jahar Bauchi

Mu cire son zuciya da bakar akidar siyasa muyi duba ga ‘Yan takarar kujerar kujeran Gwamnan jahar Bauchi, wanene cikinsu wanda ya keda manufofi, Tsare-tsare da niyar inganta rayuwar al-umman jahar?

Wanene cikin yayi ayyukan mahadi katura daga samun damansa? sannan waye mai kyakkyawar mu’amala da al’ummomi daban-daban?

Muddin mukayi wannan nazari toh la-shakka zamu kaucewa tarin matsalolin da muka hadu dasu abaya a Jahar Bauchi.

DOWNLOAD MP3

A don haka, Maigirma Sanata Bala Abdulkadir Muhammad (Kauran Bauchi) yafi duk wani mai neman takaran kujeran Gwamna a jahar Bauchi chanchantar zamowa Gwamman jahar Bauchi karo na biyu.

La’akari da ayyukan alkhairi daya gudanar wa al-umman jahar na zahiri kuma suka gamsu da ayyukan daga ransar dashi amatsayin Gwamnan jahar Bauchi zuwa yau.

DOWNLOAD ZIP

Bisa wannan dalilai yasa yazamo hakki ga duk wani mai kishin jahar Bauchi cikin zuciyarsa ba abaki ba kawai, daya kara bada dama wajen dangwala Kuri’arsa wa Kauran Bauchi Karo na biyu don cigaba da ginawa al-umma Sabuwar jahar Bauchi.

Kana, muna da kyakyawar Fahimtar cewa in sha Allahu idan yakoma karo na biyu zamu samu cigaba a jahar Bauchi fiye dana yau, saboda shi KAURA jahar ce a zuciyarsa ba kamar sauran Yan-takarkarun ba da sukazo da BUGUZUM wa al-umman jahar, wasu kuma neman suna ne yakawosu ba takara ba, la’akari da irin rashin iya mu’amala da mutunta al-umma da basa dashi.

Muna rokon Allah yatabbatar wa KAURAN BAUCHI nasaran lashe zabe karo na biyu cikin sauki, ya kuma bashi ikon gyara duk kura-kuransa don cigaba da inganta rayuwar al-umman jaha, Amin Ya Allah.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button