Labaran Yau

Bidiyon Gidan Beni Meh Hawa 7 Daya Ruguje A Legas

Gidan sama meh hawa 7 ya ruguje a legas

Wani sabuwar gini meh hawa bakwai wanda aka kusa kammalawa ya fadi ya ruguje jiya a banana island dake birnin legas.

Mutane 7 bakwai ne suka tsira da rayukansu a bayanan da menama labarai suka samo.

Manema labarai sun taru a kofar wurin domin shiga su san takamanman meh ya faru, amma wajen yana kulle an hana kowa shiga.

A hiran da akayi da jami’in TVC, ya bayyana cewa ya samu labarin ginin karan kanta bata samu amincewar gwamnati ba Kamin aka fara.

Tattaunawar Jami’an TVC a yourview, sun bayyana cewa akwai ha’inci cikin lamarin gini wanda ya shafi halayyan mutane wajen rashin gaskiya da abinda yakamata saboda san zuciya yasa irin hakan keh faruwa.

Sun yi kokari nuna yatsa wa gwamnati, saboda gwamnati takeda hurumin kula da Duk wani ginin da za ayi a jihar.

Akwai hukumomi guda hudu zuwa biyar wanda suke lura da lamarin gini wanda sun kushi: Lagos e-planning permit wanda keh karkashin ministirin gine gine da cigaban birnin, hukumar kula da gine gine da tsare tsare ta jihar legas, hukumar amincewar tsare tsaren gine gine na jahar legas da sauransu wanda yakamata ace sunyi aikinsu Kuma an samu akasin haka, cewar jami’an TVC.

Ga Bidiyon Daga Bisani

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button