Ministan Ilimi Ya Ce Koh Wanne Yaro Dan Kasa Zaiyi Karatu
Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen ganin ta magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta, yana mai cewa ba ya son wani dan Najeriya daya da ya ci gaba da zama cikin rashin samun Ilimi na kwarai.
“Muna da umarnin shugaban kasa kuma muna da namu kudurin magance wannan lamarin kuma, a makonni masu zuwa, za mu jawo hankalin jama’a kan matakan da hanyoyin magance su. Ba za mu kyale duk wani cikas a yunkurin mu na cimma wannan burin ba,”
Dangane da bayanai na karya da ake yadawa, ministan ya ce yara miliyan 10.5 ne suka bar makaranta sakamakon wasu dalilai. Gwamnatinnan a shirye take wurin mayar da su makaranta sannan kuma a halin yanzu ma aiin da mukayi kenan, kuma zamu samu nasara.