Labaran Yau

UNICEF Ta Bada Gudumawar Abincin Gina Jiki Wa Yara Da Masu Ciki A…

UNICEF ta bada gudumawar abincin waraka da Gina jiki wa yara a bayelsa

Hadakayyar kasashe da Asusun kudaden yara UNICEF, ta bada taimakon abincin Gina jiki wa mata masu ciki a jihar bayelsa.

Sunyi kyautar ne a karamin asibiti wanda keh karamar hukumar Sagbama dake jihar bayelsa.

Jagoran, Unicef na ofishin patakot Anselem Audu, wanda ya jagoranci jami’an UN, sun bayyana cewa taimakon anyi ne don maganace matsaloli irin na rashin abinci Mai Gina jiki wa yara a wannan wuraren.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Jami’an UNICEF din sun samu Rakiya na jami’an hukumar lafiya ta jihar bayelsa zuwa kauyan sagbama.

Hukumar labarai ta Najeriya sun fadi cewa bincike ya nuna karamar hukumar sagbama Suna daga cikin wanda suka fuskanci matsalar ambaliyan ruwa, wanda yakai da wahalan da suka tsinci kansu ciki har suka rashin abincin gina jiki wa yaransu.

Domin magance matsalar rashin abincin, Minista Audu yace UNICEF Tana iya kokarinta dan Ta magance matsalar yanda tayi kokari a wajajen dasuka samu matsalar ambaliya su ma a jihar.

Taimakon yace da suka yi ba shi ne nafarko ba a fadin jihar bayelsa tunda aka fara ambaliyan a shekarar 2022.

Audu yace abincin gina jikin ana tsara yadda ake amfani dasu ne dan kiyayewa da magance matsaloli ta rashin isheshshen gina jiki.

Abincin gina jiki Tana maganin cututtuka dayawa a jikin yara duk da hakan likita ne keh iya fadan irin abincin gina jiki da yakamata a bawa yara in sun samu wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button