Labaran Yau

Kasar Saudia, Amurka, Iran Da Wadansu Kasashe Sunyi Magana Kan Wanda Ya Kona Al Qur’an A..i

Kasar Saudia Amurka Iran Da Wadansu Kasashe Sunyi Magana Kan Wanda Ya Kona Al Qur’ani

Wani saurayi sanye da fararen abun sauraro na kunne, dauke da tabar sigari a bakin sa ya yayyaga alkurani a ranar Larabar da ta gabata tare da cinna masa wuta.

Kasashe da yawa sun yi alla wadai da kona Quranin da wani Salwan Momika dan asalin kasar Iraqi wanda yake da zama a kasar Sweden a halin yanzu.

Wannen abu na Allah wadai ya faru ne a gaban Babban Masallacin Stockholm a yayin da musulmai suka taru domin yin Sallar su ta bbabr Idi.

Labarin Aljazeera ya ce Mr, Momika ya kutsa cikin yansanda riqe da tutoci guda biyu na kasar Sweden din a lokacin kuma taken kasar ke gudanan.

Sanye da abun kunnen nasa na sauti, rike da tabar sigarin a bakin sa ya kacalcala Quranin tare da cinna masa wuta kamar yadda jaridar ta Rawaito.

Mutumin da ya nemi kasar ta hana amfani da qurani a kasar bayannan ya yar da quranin a kasa sanna ya tattaka shi da kafar sa, wani da ke tare da shi yayi wa mutane magana cikin lasfika.
Yan sandar kasar Sweden din sun kama wanna mutum inda suka rufe shi amma sai suka sake shi bayan wata kotu a kasar ta bada umurnin sakin na sa da kafa hujja da cewa yin haka ya zama keta hakkin wannan mutum.

Daruruwan yan kasar Iraqi sunyi zanga zanga a ofishin Jakadancin Sweden din da ke Baghdad bayan aukuwar abun a Stockholm. Rahotanni sun tabbatar cewa masu zanga zangar sun kona tuta mai kaloli daban daban a lokacin zanga zangar sannan kuma wasu na dauke da Qurani da kuma hoton daya daga cikin manyan Maluman su na Shia wanda ake kira da Moqtada Al-Sadr kuma suna iface iface.

Kasar Turkiyya wanda ke goyon bayan Kasar Sweden din ta shiga NATO tayi Allah wadai da wannan abu sannan kuma ta ceh Sweden din ta sake duba abun.

Zamu koyawa wa Turawannan hankali da kuma nuna masu cewa baya daga cikin kyautawa yin haka ko kuma wasa da addinin mutane haka nan da fitsaranci.
Kasar Morocco ma tayi Allah wadai.

Ita kuma Kasar Iran cewa tayi abu ne da ka iya tada tarzoma, kuma basu yadda ba.
Itama Kasar Iraqi ta kira Jakadan Sweden din da ke kasar ta sun gana.

Saudia kuwa cewa tayi wadannan halaye na nuna tsana, baza su taba yadda da shi ba bisa ko wanne irin dalili wanda bararo ke nuni da matsanancin tsana,warewa kuma kai tsaye ya ci karo da kokari na duniya wurin yada Hakuri, Juriya, daidaito da kuma mutunta alaqar kasashe da garuruwa.

Kasar Jordan ma ta gayyaci Jakadan Sweden din da ke kasar tare da nuna masa tsananin rashin yadda da wannan aika aika da ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button